Barcelona Ta Kafa Sabon Tarihi A Laliga

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Barcelona ta yi nasarar cin kungiyar kwallon kafa ta Eibar 2-0 a wasan mako na 24 a gasar cin kofin La Liga da suka kara a ranar Asabar.

Luis Suarez ne ya ci wa Barcelona kwallon farko a minti na 16 da fara wasa, kuma kwallo ta 17 da ya ci a kakar shekarar nan, sannan Jordi Alba ya ci kwallo ta biyu saura minti biyu a tashi daga wasan.

Eibar ta karasa fafatawar da ‘yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Fabian Orellana jan kati, shi ma mai koyar da yan wasan kungiyar, Jose Luis Mendilibar an koreshi daga bakin filin wasa, bayan da ya harzuka sakamakon korar Orellana da aka yi.

Wannan ne karo na shida da aka kori Orellana a gasar La Liga, uku daga ciki a lokacin karawa da Barcelona.

Barcelona ta yi wasa 24 a kakar La Liga ta bana ta ci wasanni 19 ta yi kunnen doki karo biyar, ta kuma ci kwallaye 61 aka zura mata kwallaye 11 ta hada maki 62.

Barcelona zata ziyarci Chelsea a gasar zakarun turai da za su fafata a ranar Talata yayinda kuma kungiyar Girona za ta ziyarci Barcelona a wasan mako na 25 na laliga a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Exit mobile version