Abba Ibrahim Wada" />

Barcelona Ta Lashe Kofin Laliga Karo Na 25 A Tarihi

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta ci kofin La Liga na 25 a kakar farko da mai koyarwa  Ernesto Balberde ya yi a kungiyar, bayan da Lionel Messi ya taimaka ta doke Deportibo La Coruna 4-2.

Messi ya ci kwallaye uku rigis a wasan da Barcelona ta yi fintinkau da ratar da ba za a kamo ta ba a teburin gasar da maki 86 a wasanta 34.

Barcelona ce ta fara shiga gaba a wasan da ci 2-0 sakamakon kwallayen da Philippe Coutinho da Messi suka zura.

Sai dai ‘yan wasan Deportibo sun tashi tsaye inda suka farke bala-balan ta hannun Lucas Perez and Emre Colak, sai dai a cikin minti goman karshe ne na wasan Messi ya zura biyu, wasan ya kasance 4-2.

Wannan shi ne kofin La Liga na 25 da Barcelona ta dauka, bambancin takwas tsakaninta da abokiyar hamayyarta Real Madrid, sannan kuma wasa hudu ya rage a kammala gasar da har yanzu ba a doke Barcelonar ba.

Wasan shi ne na farko tun bayan da Andres Iniesta ya sanar da cewa zai bar kungiyar ta Barcelona a karshen kakar nan.

Dan wasan na tsakiya mai shekara 33 ya kasance a benci lokacin da aka fara, daga baya kociyansu ya sako shi a minti na 87, in da magoya bayan kungiyoyin biyu suka yi ta masa tafi.

Ranar Lahadi mai zuwa za ta kasance dama ta karshe da Iniesta zai yi wasan hamayya na El Clasico lokacin da Real Madrid za ta ziyarci filin wasa na Nou Camp.

Bayan wasan za kuma su kara a gida da Billarreal, sannan su je Lebante, kafin karshen wasansa a Barcelona wanda Real Sociedad za su ziyarce su a Nou Camp ranar 20 ga watan Mayu.

 

Exit mobile version