Barcelona Ta Na Son Siyen Ander Herrera A Watan Janairu

Daga Abba Ibrahim Wada

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta shirya tsaf domin siyan dan wasan tsakiya na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester united, Ander Herrera, dan ƙasar sifen.

Tun lokacin da united ta siyi Nemanja Matic Herrera yasamu kansa cikin tsaka mai wuya wajen buga wasa ganin kociyan ƙungiyar yafi amfani da Pogba da Fellaini.

Mai koyar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, Enersto Ɓarɓerde ya bayyana sha’awarsa na siyan dan wasan saboda tsohon dan wasansa ne a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Athletico Bilbao.

Herrera dai yakoma united ne ashekara ta 2014 lokacin tsohon kociyan ƙungiyar, Luis Ɓan Gaal yake koyar da ƙungiyar.

Barcelona tana buƙatar siyan dan wasan tsakiya saboda tana fama da matsalar yan wasan tsakiya kuma Andre Iniesta shekaru sun farab yimasa yawa.

Barcelona dai tayi niyyar biyan fam miliyan 30 domin siyan dan wasan mai shekaru 27 a duniya wanda magoya bayan united din suke yiwa laƙabi da sabon Roy Keane.

Exit mobile version