Hukumar kula da gasar La Liga ta kasar Sifaniya ta sanar da tafka asarar kudin da ya kai Yuro miliyan 892 a kakar da ta gabata ta shekarar 2020 zuwa 2021, yayin da ta bayyana kungiyar Barcelona a matsayin wadda ta yi sanadiyar asarar sama da rabin kudin.
Hukumar ta ce rashin kokarin kungiyar Barcelona a kakar da ta gabata ta sanya asarar kashi 56 na kudaden da ya dace ta samu saboda yadda mutane suka kauracewa zuwa kallon wasannin ta saboda rashin kokari.
Rashin sayan karin ‘yan wasa da matsowa da yadda kafofin talabijin ke nuna wasannin gasar La Liga kai tsaye da kuma asarar kudaden talla na daga cikin dalilan tafka wannan asarar da aka tafka.
Kungiyoyin dake La Liga sun bayyana samun kudaden harajin da ya kai sama da Dala biliyan 4 a kakar da ta gabata, amma kuma hakan ya nuna raguwar sama da kashi 24 na kudaden da aka samu a shekarar 2019 zuwa 2020 duk da matsalar annobar Korona da aka samu.
Hukumar ta ce wannan shi ne karo na farko da aka samu irin wannan asarar tun daga shekarar 2012, sai dai Hukumar ta ce tana fatan ganin ta farfado nan da shekaru 2 masu zuwa idan kungiyar ta ci gaba da kokari.
Masana sun danganta wannan asara da sauke Josep Maria Bartomeu daga shugabancin Barcelona a shekarar 2020 inda aka maye gurbinsa da Joan Laporta, sai kuma tafiyar Lionel Messi zuwa PSG ba tare da biyan ko sisin kwabo ba.
Laporta a watan Satumbar bara ya ce kungiyar Barcelona na fama da bashin da ya kai yuro biliyan guda da miliyan 350.