Abba Ibrahim Wada" />

Barcelona Za Ta Dauki Dan Wasan Liverpool Alberto Moreno

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tana dab da kammala siyan dan wasan bayan kungiyar Liverpool, Alberto Moreno, wanda yake son barin kasar Ingila sakamakon rashin buga wasanni akai akai.
Moreno dai yana buga shekararsa ta karshe a kungiyar Liverpool bayan da kungiyar taki kara masa sabon kwantaragi sakamakon kociyan kungiyar baya amfani dashi a wasannin kungiyar tun lokacin da mai koyarwar, Jurgen Klopp yazama mai koyar da Liverpool din.
Kungiyar kwallon kafa ta Lazio ce dai take zawarcin dan wasan mai shekara 26 a duniya sai dai a halin da ake ciki yanzu, Barcelona tafara tattaunawa da dan wasan dan asalin kasar Sipaniya domin ya koma Nou Camp da buga wasa.
Wasu jaridu a kasar Sipaniya ne suka bayyana cewa Barcelona tana son dan wasan wanda wasanni hudu kacal ya buga a wannan kakar domin ya dinga taimakawa dan wasanta na baya Jordi Alba.
Sai dai idan har ana maganar buga wasanni Moreno zaifi samun wasanni a SS Lazio amma kuma abune mai wahala Barcelona ta nemeshi ace bai jeba saboda girman kungiyar da kuma ganin zai iya lashe kofi idan yaje.
Liberpool dai ta siyi Moreno daga kungiyar kwallon kafa ta Sevilla a lokacin tsohon kociyan kungiyar Brendan Rodgers sai dai tun bayan tafiyar Rodgers dan wasan ya daina samun wasanni kamar yadda yake samu a baya.

Exit mobile version