A satin da ya gabata ne kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta ce za ta gurfanar da tsohon dan wasanta, Neymar, a gaban kotu, saboda abinda ta kira biyan sa kudaden da su ka wuce kima da su ka kai Dala miliyan 12 lokacin da ya ke buga wa kungiyar wasa.
Jaridar El Mundo da a ke wallafawa a kasar ta Spain ta ruwaito cewar, Neymar, wanda ya yi wasa wa kungiyar Barcelona tsakanin shekarar 2013 zuwa 2017, ya karbi kudaden da su ka wuce kima daga kungiyar a matsayin albashi.
Rahotanni sun ce, dan wasan na Brazil na daga cikin sahun farko na ’yan wasan da su ka kauce wa biyan haraji a Spain, inda a ke bin sa bashin sama da Yuro miliyan 34.5, wanda hakan ta sa har hukumomin kasar su ka gurfanar da shi a gaban kotu.
Sai dai tsohon dan wasan kungiyar sannan tsohon dan tawagar Brazil, Rivaldo, ya bayyana cewa, babban abin kunya ne idan a ka ji kungiya mai girma kamar Barcelona ta na shari’a da tsohon dan wasanta, Neymar, a kotu.
Rivaldo ya ci gaba da cewa “Idan akwai wani abu tsakanin Barcelona da dan wasan yakamata su zauna su san abinda yakamata domin a warware matsalar sannan kuma har Neymar zai iya sake komawa kungiyar a nan gaba”
Daman dai hukumomin kasar Sipaniya suna gudanar da bincike akan lokacin da Neymar yaje Barcelona da kuma tafiyar sa PSG sannan wata Kotu a kasar ta bukaci Neymar da ya biya Barcelona yuro miliyan 6 da dubu 790,000.
Sai dai har yanzu dan wasan bai ce komai ba akan wadannan maganganu da akeyi a ya yinda yake ci gaba da jinyar ciwon daya samu a kafarsa kuma a kwanakin baya kungiyar ta PSG ta bayyana cewa zata karawa dan wasan sabuwar yarjejeniya.
A shekarun da suka gabata dai Barcelona taso ta sake sayan dan wasan daga PSG sai dai daga baya cinikin bai kasance ba sakamakon kudin da PSG ta bukata Barcelona ba zata iya biya ba kuma tun kafin bullar cutar Korona ma.