Abba Ibrahim Wada" />

Barcelona Za Ta Taya Rashford Fam Miliyan 100

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta saka dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford acikin jarin ‘yan wasan da zata nema a kakar wasa mai zuwa kuma ta shirya biyan kudi fam miliyan 100 idan har United din zata siyar da dan wasan.
Rashford dai ya taso acikin karamar kungiyar inda kuma daga baya ya kasance daya daga cikin jerin manyan ‘yan wasan da United din take ji dasu a wannan lokaci sai dai kungiyar tana kokarin ganin ta kara masa sabon kwantaragin da zai cigaba da zama.
Tuni wasu rahotanni suka bayyana cewa kungiyar Barcelona ta shirya taya dan wasan fam miliyan 100 idan an kammala kakar wasa sai dai abune mai wahala kuma Manchester United din ta amince da cinikin.
Kawo yanzu dai Rashford kwantaragin shekara biyu ya rage masa a Manchester United kuma tun kwantaragin farko da dan wasan ya saka a kungiyar har yanzu bai sake sabuwar yarjejeniya ba.
Barcelona tana neman dan wasan da zai maye mata gurbin dan wasanta na gaba Luis Suares kuma tana ganin kamar Rashford shine matashin dan wasan da zai dade yana buga mata wasa kuma yana yawan cin kwallaye.
Tuni Manchester United ma ta ware makudan kudade domin kara karfin tawagar ta a kakar wasa mai zuwa bayan shugabancin kungiyar ya tabbatarwa da Ole Gunner Solkjaer aikin kungiyar na din-din-din.

Exit mobile version