Sabo Ahmad" />

Barden Madaki Ya Zama Shugaban Kungiyar Dattawan Asibitin Jihar Kano

Kungiyar dattawan asibita jihar Kano ta zabi Barden Madakin Kano, Alhaji Garba Baban Ladi Satatima, domin zama shugabanta.

Masu zaben sun tabbatar da cewa Bardakin Madakin ya cancanci wanna matsayi musamman saboda gudummawar da ya dade yana bayar  wajen raya al’umma da ci gaban kasa, a fadin jihar Kano da kewayenta, musamman ta fuskar lafiya da ilimi da wayar da kan al’umma.

Kafin wanna zabe na sa, Barden Madakin shi ne shugaban kaungiyar dattawan Asibitin Kwararru na Malam Aminu Kano da ke BirninKano. kasancewarsa shugaban dattawan asibitin na Murtala ya taka muhimmiyar rawa, wajen tabbatar da cewa, an yi wo fafaitika a wajen asibitin yadda aka bunkasa shi Daga nan ne aka lura da irin gudummawar da yake bayarwa ta fannain kula da lafiyar al’umma aka ba shi wannan matsayin na shugana jihar Kano baki daya.

Tare da shi an zabi Dakta Muhammad Lawal wanda zai tainaka masa da Alhaji Garba Aliyu sakataren kungiyar.

Haka kuma lokacin da aka gudanar da wannan zaben an zabi shugabannin na shiyoyi uku da ake da su a jihar Kanon. Alhaji Aminu B. Usman shi ne shugaban  shiyya ta tsakiya, sai  Alhaji Muhammad Nalado shugaban shiyyar Kudu ya yin da Umar Abubakar ya zama shugana shiyyar Arewa.

Da yake mayar da jawabi jim kadan bayan kammala zabar na su, Barden Madakin ya gode wa dukkan wadanda ke ba shi goyon baya wajen ganin ya samu nasarar tafiyar da mulkin nasa, wanda ta kai shi a yanzu zama shugaba na jiha

Saboda haka ne ya sake kira ga abokan aikin nasa da cewa kada su gajiya, su ci gaba da taimakon junansu yadda za su samu nasara aiwatar da aikinsu kamar yadda ya kamata.

A karshe, ya tabbatar da cewa, wannan zabe da aka yi masa zai kara masa karfin gwiwar ci gaba da bayar da gudummawarsa musamman ta fuskar lafiya a dukkan fadin jihar Kano.

 

Exit mobile version