Mohammed Bala Garba" />

Barebari Da Al’adunsu Na Aure

Barebari

Gabatarwa:

Kanuri suna ne na wata ƙabila daga cikin manyan ƙabilun Arewacin Najeriya, waɗanda suka taɓa kafa ɗaya daga cikin dauloli guda biyu mafiya girma a duk faɗin Afirka ta yau.

Mutane ne da suka samo asali daga Yemen (Abubakar, 2017; Bello, 1974). Suna da matuƙar riƙo da al’adunsu na gargajiya, addini, karɓar baƙi da kuma uwa-uba hidimtawa Alƙur’ani da masu hulɗa da shi da suka shafi koyo, koyarwa, hadda, rubutawa da kuma masu karanta shi. Babban garin su; wato Maiduguri, ana yi masa kallon matsugunni ko kuma masaukin mahaddata da kuma makaranta Alƙur’ani. Akwai wata kalma ko kuma lambar girmamawa da suke bai wa duk mutumin da ya ƙware matuƙa wajen karanta Alƙur’ani; Goni wanda da Hausa ake cewa Gwani. A wata tattaunawa da muka yi da wani matashi mai suna Ibrahim Hassan a ranar Talata 3 ga Yuli, 2019 a Tsangayar Goni Muhammad Sa’adu Ngamdu, ya shaida mana cewa, idan mutum ya je irin guraren zaman hira da matasa ke taruwa a garin Maiduguri, a mafiya yawa daga cikin irin waɗannan guraren akan samu mutum ɗaya daga cikin matasa goma da yake mahaddacin Alƙur’ani ne. Maganar da ya faɗa tare kuma da ƙarfafa ta da cewa, “Kuma hadda cikakkiya ba kame-kame ba.”

Daga cikin kyawawan al’adun Kanurai ababen ambato akwai girmama na gaba, zaman lafiya da kuma haƙuri da juna. Cibiyar Zaman Lafiya; wato Home of Peace (Wikipedia, 2016; Sean, 2013; Naijaface, 2010), a Turance, ita ce inkiyar da ake yi wa jihar Borno wadda take ita ce babbar Jihar Kanurai.

Asalinsu:

Magana mafi shahara ita ce cewa, Kanurai mutanen Yemen ne. Dakta Babagana Abubakar, ya faɗa a cikin muƙalarsa ta Turanci, Kanuri Complete, wadda aka wallafa a shekarar 2017 a shafin Intanet na Mujallar Ƙasa-da-ƙasa mai suna Research Gate, cewa: “Kanurai sun zo ne daga Zirin Yankin Larabawa (Arabian Peninsula) sannan suka zauna a wani guri mai tazarar kusan kilomita 640 daga Arewacin Tafkin Chadi wanda daga baya ya zama ƙasaitacciyar daular Kanem-Bornu.”

Sannan kuma Sarkin Musulmi Muhammad Bello (1974), ya ce: “Waɗannan Barebarin, ragowar Barebarin da suka rayu ne a tsakankanin ƙasashen Arewacin Afirka da kuma Habasha.  Su ne waɗanda Humayyar (sunan ƙabila ne) suka kora daga Yemen…” Wanda kuma a ƙarshen bayanin nasa ya ƙare da cewa: “…Sannan suka gangaro Kanem, suka zaune ta…”

A cikin wata tattaunawa da muka yi da Dakta Shekarau Angyu, Masa-Ibi, Aku-Uka na Wukari, a ranar Asabar 19/08/2017, a fadarsa da ke Wukari, ya shaida mana cewa: “Asalinmu daga Yemen ne. Mun taho tare da ‘yan’uwanmu Kanurai muka rabu da su a Ngazargamau.”

 

Rabe-rabensu:

A farkon lamari, Yaren Kanuri kala ɗaya ne tal! Amma sannu a hankali sakamakon yanayin siyasar rayuwa da ta haddasa gaurayuwar Kanurai da wasu baƙin yarurrukan ko dai ta hanyar zuwansu garuruwan Kanurai ko kuma zuwan Kanurai wasu garurwan, ya haifar da hayayyafar wannan yare inda har ta kai ga an samu bambamce-bambamcen wasu kalmomi ko kuma ma canjin yaren kaco-kaf. Daga cikin rabe-raben Kanuri akwai; Wuje, Gumati, Manga, Bodoi, Kanembu, Morr, Kwayam, Suwurti, Buduma da sauransu.

 

Addini:

Kanurai mutane ne Musulmai. Dakta Babagana Abubakar ya ce: “100% ɗin Kanurai Musulmai ne waɗanda suka riƙi addinin Musulunci a matsayin tafarkin rayuwarsu sannan kuma Annabi Muhammadu samfurin su…”

 

Al’adunsu Na Aure:

Hakika Kanurai suna daya daga cikin kabilun da suka fi kowani kabila iya rukon aure da gudanar da al’adu a yayin aure. Al’adun nasu sun hada da:

Bawaram

Fafurai

Wushe-wushe

Klatul

Kalawa

Ka’aji

Humram

Kulaicam

Kalam-wuri

Kndai

Kususuram

Wushe – wushen yaa’ye

Nalle

Tulur

Ksai lewa

Kaulu

Ganga-kura

 

Bawaram:

Kalmar Bawaram tana nufin babanni. Idan kuwa a aure ne aka ce Bawaram, to ana nufin kayayyakin da ango yake yiwa dangin amarya, wadanda suka hada da:

Ya – uwa

Kamu ba’aye – matar uba ko kuma matan uba

Bawa – kannen uba da yayunsa

Yakura – babbar yayar amarya

Am ngawoye – mutanen baya

Duhuram – mai kitso

Ka’aram – kakanni

Ya njimma – uwar daki.

 

Fafurai:

Wani akwati ne da gidan amarya suke yiwa ango. Abubuwan da ake sakawa a cikin akwatin sun hada da, shaddodi da yadudduka da huluna da sallaya da turare da agogo da takalmi da sauransu.

 

Wushe-wushe:

Biki ne da ake gudanarwa tsakanin bangaren amarya da na ango ana gobe daurin aure. Bangarorin biyu su kan yi shigar al’ada irin ta Kanurai su hadu a wani farfajiya ko kuma su kama hotai domin yin wannan bikin. A wajen bikin, ana kebe amarya da ango akan kayatacciyar kujera, yayin da makadan gargajiya ke kida, ‘yan mata da samari suke rausayawa irin ta al’ada a gaban ango da amarya. Daga nan kuma sai a shiga yiwa ango da amarya kari tare da daukar hotuna. Wushe – wushe yana daya daga cikin al’adar Kanurai wanda kabilu da dama suka ara suke gudanarwa yau a Nijeriya.

 

Klatul:

Yana nufin wanke kai, mata kadai ake yiwa. Ana yinsa ne idan aure ya saura kwana uku. Yadda ake yin shi ne, babannin amarya ne suke wanke kan amarya da ruwan karkashi. Bayan an kammala wanke kan, ana yin kidan kwarya; wanda tsofaffin mata suke waka cikin harshen Kanuri. Shi wannan kidan kwaryar, ana yinsa tamkar irin wanda aka san Hausawa ne da shi.

 

Kalawa:

Tamkar shadi yake, sai dai shi ba bugu ake yi ba. Yadda ake yinsa shi ne, ana tanadar akushi da bushasshen karkashi da farar shinfida, sai a zo da ango ko amarya a daura akan wannan shinfidar, daman an daura tuwon buski ko shinkafa akan wuta, ana saukewa za a debo shi da zafinsa, sai ango ko amarya su bude tafin hannunsu, a zuba musu akai da zafinsa, sai su kuma (amarya ko angon) su juye abincin da aka zuba musu a tafin hannu a cikin wannan akushin. Ana yin haka har sau uku, sannan sai a goge musu hannayensu, a shafe musu bushasshen karkashin. Daga nan sai ‘yan uwa da abokan arziki su zo suyi musu kyaututtukan alfarma. Idan da wanda zai yi kyautar gida ko mota ko kuma jari, to a wannan wajen zai yi. Ma’anar yin wannan al’adar shi ne, yadda suka rike wannan abincin da zafinsa, Allah ya sa su rike wannan auren fiye da haka.

 

Kalaji: Yana nufin turaren wuta. Ango ne yake bada kudin sayen turaren wuta wanda amarya take zuwa da shi dakinta. Wannan ma yana daya daga cikin al’adar Kanuri wanda sauran kabilu suka ara ayau.

 

Humram:

Wani turare ne na ruwa wanda mata suke shafawa a jikinsu. Shi ma ango ne yake bada kudin sayen sa.

 

Kulaicam:

Shi ma nau’in humram ne, sai dai shi da man shafawa ake hadawa, a shafe jiki. Shi ma ango ne yake bada kudin sayen sa.

 

Kalam-wuri:

Wuri kudi ne na da (baya) da ake amfani da shi. Kalam – wuri wani abu ne karami kamar kafbasa, wanda ake manne shi da kudi gaba dayansa a baiwa amarya ta tafi da shi dakin mijinta a matsayin kyauta. Duk lokacin da bukatar kudi ya sameta kuma babu kudi a hannunta, sai ta daye wannan kudin da ke like, tayi uzurinta da shi. Ita wannan al’adar, takwarar amarya ce take yi, idan kuwa ba ta nan (ta mutu), sai ‘ya’yanta ko ‘yan uwanta su yi.

 

Kndal:

Kalmar Kndal asalinta Kanuri ce. Kndai wani dan kwano ne ko kuma akushi da ake saka shi da kaba (da Hausa sunansa Adudu). Ana yi masa ado, sai zuba goro da fure ko dabino a ciki amarya ita take zuwa da shi gidanta. Idan mijin mai cin goro ne, sai ya yi amfani da shi; idan kuwa ba ya ci, ita ma bata ci; sai ta dinga sa dabino ko wani abu da take bukatar ajiyewa a ciki.

 

 

Littafin Kasar Barno A Jiya na Mohammed Bala Garba

 

Kususuram:

Abin da ake nufi da Kususuram shi ne, kai kayan lefe. Yadda ake kai kayan lefe a al’adar Kanurai ya bambanta da na sauran kabilu. Idan an tashi kai kayan lefe gidan iyayyen amarya a al’adar Kanuri, ana hadawa da Tinkiya ko Sa ko Saniya. Za a daura atamfa a wuyan Tinkiyar ko San, ko Saniyar a yayin da za a kai kayan lefen. Wannan atamfar da aka daura a wuyan dabbar, idan an je gidan iyayyen amarya, suna ba da ita kyauta ga wanda ko wadanda suka rike dabbar a yayin kai kayan lefen.

 

Wushe-wushen Yaa’ye:

Ana yinsa ne a ranar Alhamis. Yadda ake yi shi ne: dangin amarya ne za su hadu su yi nakiya, a yayin da bangaren ango kuma za su kawo musu goro tare da yi musu sannu da aiki; sai bangaren amarya su ba su wannan nakiyar da suka yi.

 

Nalle:

Yana nufin lalle ko sa lalle, ana yinsa a ranar Talata. Bangaren ango za su kai buhun lalle da cingam da minti har ma da goro da dai sauransu izuwa gidan iyayen amarya.

 

Tulur:

Kalmar Tulur a Kanuri yana nufin bakwai. Shi Tulur a auren Kanurai kuma, yana nufin zaman bakwai da mace daya ko biyu suke yi a gidan amarya na tsawon kwanaki bakwai. A wannan zaman, wadannan matan su za su rika yiwa amarya girki da shara da wanke-wanke da dai sauran hidindimun cikin gida har na tsawon wannan kwanaki. Bayan kwanakin sun cika, ango yana yiwa wadannan matan kyautar atamfa da sabulai da turare, wanima har da ‘yan kudade.

 

Ksai lewa:

Gaisuwan iyayye. Ana yinsa ne a washegarin daurin aure, inda ango da abokanansa za su kai ziyarar gaisuwa zuwa wajen iyayyen amarya.

 

Kaulu:

Ango kadai ake yiwa; yadda ake yi shi ne, ana dama karkashi ne da ruwa, sai mahaifin ango, ko kanin mahaifinsa, kai wani lokacin ma maigidansa na wajen aiki ko sana’a ne zai shafe masa hannunsa da wannan ruwan karkashin. Wannan fata ne na duk abin da ya mallaka ya yaukaka (wato yayi albarka).

 

Ganga-kura:

kidan gargajiya ne da ake yinsa ranar daurin aure. Dangin amarya ne da na ango maza da mata za su hadu suyi shiga irin ta al’ada su fito su rausaya a tsakanin juna.

Wadannan su ne al’adun Kanurai a bangaren aure a takaice, wanda muka kawo su a cikin littafin ‘Kasar Barno A Jiya’.

Wadannan al’adun suna daga cikin jigon da ya sa Kanurai suka fi kabilu da dama juriya wajen rukon aure. Sai dai kuma a wani bangaren, wasu na ganin wadannan al’adun suna daga cikin abin da ya sa auren Kanurai yake da tsada ayau, duk da cewa ba dukkan Kanurai ba ne suke gudanar da wadannan al’adun ayau, saboda yanayin da ake ciki.

Da wannan muka zo karshen wannan mukalar tamu ta yau akan Kanurai da al’adun na aure. Akwai bayani iya bakin gwargwadona game da tarihin kasar Barno, suna, asali, da kuma wasu daga cikin kyawawan halayen Kanuri da abin da ya shafe su a littafin KASAR BARNO A JIYA.

Muna rokon Ubangiji Allah Madaukakin Sarki ya albarkaci wannan aikin namu, ya sa ya amfani dukkan ‘yan uwana abota ilimi.

A karshe muna sake rokon Ubangiji Allah Madaukakin Sarki ya ba mu zaman lafiya mai daurewa a kasarmu ta Nijeriya. Amin summa amin.

 

Garba dalibi ne a Jami’ar Maiduguri. Za a iya samun sa a wadannan lambobin: 08098331260, 08025552507.

Exit mobile version