Connect with us

MANYAN LABARAI

Barin Aski Da Yanke Farce: Ba Tilas Ga Mai Layyya – Sheikh Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil, Shugaban Majalisar Malamai na Kasa reshen Jihar Kano ya bayyana cewa, Musulunci bai tilasta wa Musulmi mai niyyar layya barin yin aski da yanke farce ba, kamar yadda da yawa su ka dauki hakan da zafi.

Shahararen malamin addinin Musuluncin na jihar ta Kano kuma babban manomi ya yi wannan fatawar ne a wani gidan rediyo mai zaman kansa a jihar ranar Asabar da ta gabata, 25 ga Yuli, 2020, a cikin wani shiri na bayar da fatawowoyi da misalin karfe 11:00 na dare.

Sheikh Khalil ya ce, babu wanda ya tilasta ko wajabta ga kowanne mutum Muslumi da ya ke da niyyar yin layya, barin yin aski ko yanke farcensa, ya na mai cewa, ko wane mutum ya na da dama da iko kuma bai yi laifi ba idan ya yanke farcensa ko ya yi aski, idan watan Zhul Hijjah ya kama gabanin ranar Babbar Sallah.

Sai dai kuma Malam ya kara da cewa, barin aski da yankan farce ga mai niyyar layya mustahabi ne, wato abin so ne, amma ba wajibi ba, tilas ba, kamar yadda wasu wadanda ba malamai ba su ke zafafa abin a wannan lokaci.

Shugaban majalisar malaman na Jihar Kano kuma dan siyasa ya cigaba da cewa, da yawa mutane, da yawan mutane su na zafafawa, kamar sabo ne, inda za ka ga su na daukar abu su ba shi mahimmanci da bai kai su ba shi ba, kuma abu muhimmi su ki ba shi mahimmancin gaske, kamar yadda yakamata, inda shehun malamin ya bayar da misalin sallolin nafila na Shafa’i da Wuturi, ya na mai cewa, za ka ga mutum bai damu da sallar Shafa`i da Wuturi ba, kuma idan a ka yi rashin sa’a su ne masu zafafa irin wannan mustahabi na sai ka bar aski da yankan farce da zarar watan Zhul Hajjih ya kama, alhalin hakan mustahabi ne, ba dole ba.

Ya ce, “duk da hadisai sun zo da abin, kuma abu ne mai kyau, amma ba dole ba ne.”

Har ila yau Sheik Khalil ya ce, Shafa’i da Wuturi muhimmin abu ne a Musulunci, domin a na ganin idan mutum ba ya yi kwatakwata, to ba za a sa shi a cikin mutanen kirki masu nagarta ba, wanda a na ganin cewa shaidarsa ma ba za a karba ba a fahimta ta Imamu Malik.

“Amma sai ka ga abu muhimmi irin wannan ba a ba shi muhimmanci ba, sai wani abu daban,” a ta bakin Sheikh Khalil.

Ya kara da cewa, “haka kuma ya kara da cewa, ya na daga cikin alamomi na rashin nagartar al’umma ta fifita abu da ba muhimmi ba, ta maida shi muhimmi ko kuma muhimmi a maida shi ba mahimmi ba. A irin wannan ne za ka ji cewa, da an ga ba ka azumin Litinin da Alhamis ko tara ga Zhul Hijjah ko ka yanke farce ko ka yi aski a wannan lokaci sai ka ji wani ya ce, ‘ba za ka yi layya ba ne?’ da dai sauran maganganu, wadanda ba malamai ba ke zafafawa a gabobin addini daban-daban irin wannan, duk da yawaita ibada ta sadaka, kyauta, azumi, zikiri, karatun Alkurani da sallolin nafila da sauransu, abu ne da a ke son su a wannan wata na Zhul Hijjah da ma sauran lokuta na rayuwa.”
Advertisement

labarai