Connect with us

WASANNI

Barin Madrid Abu Ne Mai Sauki, In Ji Ronaldo

Published

on

Cristiano Ronaldo ya ce yanke shawarar rabuwa da kungiyar Real Madrid tare da komawa Juventus, na daga cikin matakai mafiya sauki da ya dauka a rayuwarsa.

Ronaldo mai shekaru 33, ya yi wannan furuci ne a lokacin da yake zantawa da wata kafar yada labarai a Italiya, inda ya bayyana matukar mamakin ganin irin karrama shi da magoya bayan kungiyar Juventus suka yi a Turin.

Bayan shafe shekara da shekaru a Sipaniya Ronaldo ya taimakawa Real Madrid samun nasarar lashe kofin gasar zakarun kungiyoyin nahiyar turai 4, kafin daga bisani, ya yanke shawarar rabuwa da kungiyar, ya koma Jubentus kan farashin Fam miliyan 105.

A cewar Ronaldo bai taba tunanin zai bugawa Jubentus wasa ba, amma sai gashi a kungiyar sai dai kuma baya dana sanin hakan saboda Juventus babbar kungiya ce kamar Real Madrid.

A cewar dan wasan ba shakka ya samu dimbin nasarori a Real Madrid wadanda yake mutuntawa, sai dai a halin yanzu abubuwa ne da suka shude

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: