Connect with us

DAGA NA GABA

Barista Hadiza Dije Ali: Gwarzuwarmu Ta Mako

Published

on

Maasaniyar ilimi,
Kwararriyar masaniyar tattalin ariziki da tsimi
Masaniyar shari’a
Fitacciyar ‘yar gwagwarmayar kungiyoyi
Mai tallafa wa marasa karfi.

Tarihinta
An haife ta ranar 19 ga watan Mayun shekara ta 1963 a Zariya, a tsohuwar jihar Kaduna, bayan iyayenta sun sa ta makarantar Allo, sai kuma aka sa ta a makarantar firamare ta ‘St’Poul’sTownship Primary School’a garin Jas inda ta kammala a shekara ta 1977, daga nan sai ta sami shiga makarantar Sakandare ta, ‘Gobernment Secondary School Zaria’, inda ta kammala a shekara ta 1983, A shekara ta 1988 ta kammala karatun ta a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, a bangaren nazarin kididdigar kudi, ta sami shaidar karamar difiloma,ba ta tsaya ba, a shekara ta 2002, ta koma bangaren nazarin shari’a na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ta sami shaidar digiri kan shari’a, sai ta zarce makarantar amincewa da zama kawararriyar Lauya, a shekara ta 2004, a kuma shekara ta 2012, ta sami shiga Kwalejin tunawa da Nuhu Bamalli da ke Zariya, inda ta sami takardar shaida na kwarewa kan kididdigar kudi, a kuma a shekara ta 2015, ta sami takardar babbar difiloma kan kididdigar kudi.

Takardun Shaidan Karatu Da Ta Ke Da Su
1.Takardar kammala makarantar firamare a shekara ta 1977,
2.takardar kammala sakandare a shekara ta 1983,
3.Karamar difiloma kan kididdigar kudi a shekara ta 1988,
4.Babbar difiloma a shekara a shekara ta 22002
5.Takardar shaidar zama kwararriyar lauya, a shekara ta 2004,
6.Karamar difilolma kan kididdiga, a shekara ta 2013,
7.Babbar takardar shaida kan kididdiga da tsimin kudi, a shekara ta 2015,
8.Kololuwar takardar shaida na zama a kungiyar masana kididdigar kudi a Nijeriya (ANAN).

Kwasa-Kwasai Kan Kididdiga Da Kudi Da Ta Halarta
1.Taro kan yadda za a yi kididdigar kudi da kuma yadda za a hana
sabarta – juyarta da kudi, wanda ta halarta a shekara ta 2009,
2.Taro mai taken mata su ne jigon ci gaban al’umma a Nijeriya, wanda
kamfanin mai na ‘SHELL’suka shirya a watan Fabrairun shekara ta 2010.
3.Takardar shaidar da ta samu na taron kara wa juna ilimi da aka shirya wa manyan ma’aikata da suke kula da bangaren kudi na Jami’ar Ahmadu da ke Zariya, wanda cibiyar ‘George Andrews and Partnes Centre For Development Of Accounting Practice’ ta shirya a watan Janairun shekara ta 2006, an gudanar da taron a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Tarurrukan da ta halarta a kasashen waje
1.Taro kan matsayin mata a fagen mulki, wanda makarantar koyon kasuwan, ‘African Bussiness School ‘ da ke Dubai ta shirya a watan Oktoban shekara ta 2009.
2.Taron kara wa juna ilimi da aka shirya na yadda ake gudanar da kungiyar manyan ma’aikata na jami’o’in Nijeriya [SSANU],taron an gudanar da shi a garin Tema na kasar Ghana, a shekara ta 2010.
3. Taro kan yadda za a kawo karshen wariyar al’umma, da aka yi a garin Turn na kasar Italiya.

Kwamitocin da ta yi aiki a cikinsu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya
1.Ta zama mamba a kwamitin ladabtar da kananan ma’aikata da ciyar da su gaba na tsangayar ilimi na Jami’ar Ahmadu Ahmadu Bello, da ke Zariya, a shekara ta 2005
2.Sakatariyar aiwatar da umurnin biyan fansho,a shekara ta 2006
3,Mamba ana yadda za a yi aiki a bangaren kudi na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, a shekara ta 2006
4.Kwamitin daukar aiki da kuma ciyar da ma’aikata gaba, a shekara ta 2006
5.Sakatariya a kwamitin sa sutura na tsangayar ilimi na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a shekara ta 2007,
6.Sakatariyar kwamitin ziyarar jami’ar Ahmadu Bello, na shekara ta 1999 zuwa shekara ta 2003 da ya shafi bangaren kudi na jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.
7.Sakatariya na kwamitin sabunta kudaden gidajen gwamnatin tarayya, daga shekara ta 1992 zuwa 1998.
8.Mamba a kwamitin biyan kudaden ayyuka ma su wuya da hadari a shekara ta 2009.
9.Sakatariya a kwamitin karban kudin makaranta, daga shekara ta 2009 zuwa 2010 da kuma shekara ta 2010 zuwa 2010 zuwa 2011.
10.Sakatariya a kwamitin kula da aikace – aikacen bangaren kudi na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, a shekara ta 2011..
11.Sakatariya a kwamitin karban bashin kungiyar NAAT da FBN, Aa shekara ta 2014.
12.Mamba a kwamitin yadda za a kashe kudin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a shekara ta 2014.

Takardun Shaida Na Karramawa Da Ta Samu
Ta sami takardun shaida daga kungiyoyi ma su zaman kan su da kungiyoyin dalibai da kuma kungiyoyin lauyoyi ta Nijeriya.

Matsayin Da Ta Ke Kai Zuwa Yau
1.Shugabar mata a kungiyar manyan ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya [ SSANU],
2.Mataimakiyar shugaba, a kungiyar kwadigo a Nijeriya, [NLC]
3.Babbar jami’ar kididdiga na cibiyar karatu na [DLS/ABU] a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: