Mariana Mazzucato, farfesa a jami’ar London, ta bayyana cikin wata mukala da jaridar The Financial Times ta wallafa a shafin intanet cewa, annobar COVID-19 ta nuna irin kurakuran dake akwai a salon tattalin arziki na jari hujja, inda ta ce akwai bukatar masu tsara manufofi su mayar da hankali kan ci gaba mai dorewa bisa daidaito, domin sake gina kasashensu.
Mukalar ta yi nuni da cewa, idan kasashen yamma na son kyautata gina kansu a shekarar 2021, to kamata ya yi masu tsara manufofi su karfafa tsarin kiwon lafiya da zuba jari a bangaren ababen more rayuwa da rage gibin akwai a bangaren amfani da fasahohin zamani da daukar darrusa daga matsalar kudi da kuma daukar ka’idoji masu tsauri na taimakawa kamfanoni, domin tabbatar da an kula tare da kare muradun al’umma, da tabbatar da tattalin arziki na kan hanyar ci gaba mafi dacewa, tana mai cewa, bisa wadannan matakai ne kadai za a shawo kan kalubale mai tsanani da jama’a ke fuskanta. (Fa’iza Mustapha)
Dabarun Gwamnatin Sin Ya Baiwa Duniya Kwarin Gwiwar Tinkarar Kalubaloli
“Abin da babba ya hanyo yaro ko ya hau kololuwar...