Mohammed Albarno" />

Barkewar Zanga-zanga A Nijeriya Na Iya Maimaita Tarihi.

Zanga-zanga A Nijeriya

A Nigerian youth seen waving the Nigerian national flag in support of the ongoing protest against the unjust brutality of The Nigerian Police Force Unit named Special Anti-Robbery Squad (SARS) in Lagos on October 13, 2020. - Nigerians took to the streets once again on October 13, 2020, in several cities for fresh protests against police brutality, bringing key roads to a standstill in economic hub Lagos. Demonstrations organised on social media erupted earlier this month calling for the abolition of a notorious police unit accused of unlawful arrests, torture and extra-judicial killings. The government gave in to the demand on October 11, 2020, announcing that the federal Special Anti-Robbery Squad (SARS) was being disbanded in a rare concession to people power in Africa's most populous nation. (Photo by Benson Ibeabuchi / AFP) (Photo by BENSON IBEABUCHI/AFP via Getty Images)

A daidai lokacin da zanga zanga na kara kamari Nijeriya, da kum irin dagewa, da jajircewa da masu zangar neman sai an dakatar da Jami’ai rundunar FSARS ta ‘yan sanda, wannan wata alama ce dake nuna cewa komai na iya faruwa kamar yadda ya auku a baya ga ‘yan Neja Delta, da kuma Biafra.

Zanga-zangar #EndSars, wanda ya fara aukuwa a farko farkon watan Oktoba na 2020, biyo bayan cikar shekara 60 da samun ‘yancin kasar. Wanda wasu fusatattun matasa, da kungiyoyi irin su Rebolution Group, da kungiyar Concern suka shirya, abin na iya tashiwa daga manufar da aka fara abin akai zuwa wata manufa ta daban.

Tun farko dai da masu zanga-zangar suka matsa lamba, tare da yin kutse zuwa Abuja da nufin kai koken su, wanda har ya kai ga samun nasarar musanya rudunar ta FSARS zuwa SWAT, amman lamarin bai wadatar ba, domin yana kara raba kan al’umnar kasar ne. Domin wasu na ganin rushe rudunar ta FARS ta kamar sake bawa ‘yan ta’adda daman cigaba da yin aika aika ne.

Kusan sama da sau uku kenan ana kaiwa masu zanga-zangar hari, wanda farkon farin ya yi sanadiyar rashin rayuka, ya faru ne a Bega dake Abuja Babban Birnin Tarayyar Nijeria, wanda wasu fusatattun matasa ‘yan gari masu goyon bayan SARS din suka fatattaki masu zanga-zangar da sara da suka, tare da bugu.

Haka zalika, kungiyoyin matasa na Arewa sun ware kansu inda suma suka fara zanga-zangar mai taken #Endinsecuritynow, yayin da suma basu tsira daga harin yan daba ba.

Wasu masana na malaman addinai na ganin wannan zanga-zangar ba dai dai bane, domin na iya haifar da matsalar da abin sai ta gagari gwamnati, wasu daga ciki har haramta zanga-zangar suke, sai dai tuni wasu daga cikin masu goyon bayan sun maida musu martani, inda suke cewa suma malaman yanzu siyasa kawai suke ba addini ba, domin kowa nasa yake dubawa, da abin ta shafe su da sai sunfi haka damuwa.

A bangaren gwamnatin kuwa, abin na neman zame musu kashin wuya, duba da irin kokari da suke yi na ganin sun dakatar abin. Shugaban majalisar tarayyar kasar sun yi zama da wasu daga cikin shahararrun mutane da ake ganin suna jagorantar zanga-zangar, irin Su Debid Adelike Dabido da sauran su, inda sun basu hakuri, tare kuma alkawarin daukar mataki. Sai dai hakan kamar ya karawa masu zanga-zangar gishiri a miya, saboda wanda bai fito ba ma ya sake fitowa, tare kuma da rufe manyan hanyoyi, irin su Lekki Toll Get, titin zuwa Idaban, sannan hanyar shiga Abuja daga Filin saukar jirgin sama.

Babban abinda ya kamata mu lura anan, idan muka yi duba da masomar rikicin Neja Delta da Gwamnatin Nijeriya, a lokacin da bututun mai ya fashe, mutane suka zo diba, sai ‘yan sanda suka hana, kana daga baya ya janyo mutuwar mutane, kana daga baya aka soma zanga-zanga, wanda akwai lokacin da za su zo Abuja zanga zanga, hayaniya ta barke tsakanin su da yan sanda, har ya kai ga kashe mutum daya, tare da kame mutanen. Daga baya manyan gari suka nemo belin su, daga baya suka kara kaimi wajen zanga-zangar.

A cigaba da zangazangar su, har ya kai ga miyagu suka shiga cikin su, wanda har ya kai ga miyagun cikin su suka fara harbin jami’an tsaro, kana saga baya abin ya zama babban matsala wanda ya haifar da yaki wanda ake cema yakin Neja Delta.

Haka zalika a Maiduguri babban birnin jihar Borno, inda a tsakanin 2008 zuwa 2009, wata kungiyar Addinin musulunci da ake kira da Salaf, wanda Muhammad Yusuf ke jagorantar su a lokacin, sun zo wucewa makabarta da gawa, yayin da lokacin Gwamnati tasa dokar saka hular kwano ga ko wanne Dan Achaba, sai dai su basu sa ba, domin suna sanye da rawuna, kuma rawani da hula ba zaiyu ba. Suma hayaniyya ta shiga tsakanin su, wanda har ya kai ga su sojojin bube wuta ga mabiyan nasu. Bude wutan ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama 25, wanda yakan shi ne silar mafarar Boko Haram.

Haka zalika, wannan zanga-zangar da ke cigaba da gudana a yanzu, na kawo karshen zaluncin ‘Yan sanda ta SARS, shima miyagun mutane na iya haduwa da masu zanga-zangar, wanda tun a farkon makon nan aka fara rasa rayuka, sannan an kaiwa Gwamnan Jihar Osun hari, an farfasa masa motocin masu yi masa rakiya, yayin da shima ya tsallake rijiya da baya. Sannan a Abuja babban birnin tarayyar Nijeriya, da marecin ranar Asabar, wata arangamar ta sake aukuwa wanda har ya kai ga kona tayoyi a kan tituna, sannan babu wanda ysan abinda zai iya faruwa nan gaba.

Zanga-zangar na iya samun bakin mutane na miyagu, wanda za su iya lalata dukiyoyi, da rasa rayuka, wanda hakan na iya zama gagarumar matsala nan gaba kadan idan gwamnatin bata kawo karshen abinda suke so a kawo musu shi karshe ba.

Abinda ko wanne dan Nijeriya yakamata ya sani, musamman jami’an tsaro da suke karkashin ikon gwamnati, komai za su yi, su yi shi cikin tsari da tunani, zama yakamata ayi da basu zanga-zangar, sannan a kawo karshen rashin tsaro a Nijeriya, da kuma kawo karshen zaluncin da hukunta mutane ba bisa ka’ida ba. Hakazalika bangaren masu zanga-zangar, su kula da su waye ne za su shigo cikin su, kar su bari saboda banbancin jam’iya ya kawo rikicin da zai iya addabar kowa. Allah ya tausaya mana, ya kuma bamu zaman lafiya, yasa a dace, Ameen.

Exit mobile version