Gareth Barry Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta West Brom, ya kafa tarihin zama dan wasan da yafi kowanne yawan buga wasannin firimiya na kasar Ingila.
Barry da ke buga bangaren tsakiya ya kafa tarihin ne bayanda da ya fafata a wasan da West Brom ta buga da Arsenal a ranar litinin, wanda shi ne wasansa na 633 da ya buga a gasar ta Premier.
Wasan na ranar Litinin, ya bai wa Barry damar shafe tarihin da Ryan Giggs, tsohon dan wasan Manchester United ya kafa, na buga wasanni 632 a gasar kwallon kafar ta Ingila.
A watan Mayu na shekarar 1988, Gareth Barry ya fara buga wasa a ingila, kuma a kungiyar Aston Billa, ya kuma bugawa kungiyar jimillar wasanni 365, sai kuma Manchester City da ya bugawa wasanni 132, daga nan ne ya koma Eberton ya buga wasanni 131, sai kuma cikon wasanni 5 da ya bugawa kungiyar da yake a yanzu wato West Brom bayan da ta sayo shi daga kungiyar Eberton akan fan din ingila dubu 800.