Basarake Mai Daraja Ta Daya Ya Kwanta Dama A Adamawa

Basarake

Daga Muh’d Shafi’u Saleh,

Sarkin masarautar Mbula a jihar Adamawa, Mai martaba Murum Mbula Cif Joel Joram-Fwa, ya rasu bayan fama da gajerar jinya, yana da shekaru 82 a duniya.

 

Rasuwar sarkin wanda magajin sarkin Murum Mbula, Mista Fenny Fwa, ya sanar ya ce ya rasu ne ranar Lahadi a babban asibitin gwamnatin tarayya dake Yola FMC.

 

Tuni dai gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana mutuwar da cewa jihar ta rasa jigon tabbatar da wanzuwan zaman lafiya.

 

Gwamnan cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in yada labaran gwamnan Humwashi Wonosikou, ya aikewa manema labarai tace gwamnan ya dimauta da samun labarin rasuwar basaraken.

 

Tace gwamnan Fintiri, ya bayyana rayuwar sarkin Mbula, da cewa ya gudanar da ita wajan kyautatawa jama’a da bautar Ubangiji Allah.

 

Tace gabadaya majalisar masarauta tayi babban rashin mai gyara da daidaita rigima da fuskantar kalubale komin girmanta da ta fuskanceta.

 

Haka kuma sanarwar ta bukaci jama’ar masarautar Mbula, iyalan mai martaban, da daukacin jama’ar jihar, da su dauki dangana, su maishe da lamarin zuwa ga Allah game da babbar rashin da sukayi.

 

Tace “mun rasa sarkin da mukeso abin girmamawa, amma mu dukufa a Adamawa muna alfahari da danmu sarki wanda rayuwarsa da ayyukansa zasu dawwama ba za’a taba mancesu ba” inji sanarwar.

 

Marigayi martaba Murum Mbula Cif Joram-Fwa, ya rasu ya bar mace guda da yaya 10.

Exit mobile version