A ranar Talata ne kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta bayyana cewa, basussu ka da ake bin Nijeriya zai iya hana wa gwamnatin tarayya samun damar bunkasa tattalin arziki. Haka kuma, OPEC ta bayyana cewa, bisa umurnin da aka bai wa Nijeriya, kasar ta rage fitar da danyen mai a kasuwan Duniya daga ganga miliyan 1.76 a kowacce rana a farkon wannan shekara zuwa ganga miliyan 1.4 a kowacce rana a watan Yuni. Nijeriya yana daya daga cikin mambobin kungiyar OPEC, wanda ta amince da rage yawan danyen mai a kasuwan Duniya domin farfado da farashin mai.
A cikin rahoton kasuwan mai da ta saba fitarwa duk wata wanda ta fitar a ranar Talata, kungiyar ta bayyana cewa, ana samun karuwar bashin da ake bin Nijeriya da kashi 15 a kowacce shikara, inda a karshen watan Maris ta shekarar 2020 aka samu karin dala biliyan 79.3. Ta kara da cewa, ana samun karuwar basukan ne a cikin gida da kuma na kasashen ketare sakamakon karancin samun kudaden shiga na cikin gida da kuma faduwar farashin danyan mai a kasuwan Duniya. OPEC ta ci gaba da cewa, duk da karuwar basukan da ake bin Nijeriya, ana samun karin fitar da kayayyaki da kashi 20, gwamnatin tarayya tana fuskantar basu ka ne sakamakon karancin kudaden shiga daga haraji.
“Sakamakon haka, bashi zai iya hana gwamnatin kasar samun damar gudanar da bunkasa tattalin arziki,” in ji kungiyar OPEC.
Sakamakon rage yawan danyan mai a kasuwan Duniya, OPEC ta bayyana cewa, a baya Nijeriya tana fitar da danyan mai a kasuwan Duniya wanda ya kai ganga miliyan 1.76 a kowacce rana, inda aka rage zuwa ganga miliyan 1.52 a kowacce rana a farkon wata ukun wannan shekarar. Ta ce, a tsakanin watan Mayu zuwa watan Yunin shekarar 2020, Nijeriya ta samu nasarar fitar da danyan mai a kasuwan Duniya wanda ya kai ganga miliyan 1.44 da kuma ganga miliyan 1.41 a kowacce rana ta Duniya. Ta kara da cewa, binciken da aka gudanar ya nuna cewa, OPEC ta fitar da danyan mai a kasuwan Duniya wanda ya kai ganaga miliyan 22.27 a kowacce rana a cikin watan Yunin shekarar 2020, kasa da ganga biliyan 1.89 a duk wata. Ta ci gaba da bayyana cewa, an rage yawan danyen mai da kasashen Saudiyya da Irak da benezuela da Daular Larabawa da kuma Kuwait su ke fitarwa, yayin da aka kara yawan danyan man da kasar Ekuatorial Guinea da Libya su ke fitarwa.
“A watana Yuni, kasashen Saudiyya da Daular Larabawa da kuma Kuwait sun kara rage yawan danyan mai da su ke fitarwa a kasuwan Duniya,” in ji OPEC.