Bashin Ilimi Ga Daliban Nijeriya: Manufar Da Ba Ta Da Kyakkyawar Manufa
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bashin Ilimi Ga Daliban Nijeriya: Manufar Da Ba Ta Da Kyakkyawar Manufa

byAlhaji Adamu Rabiu
2 years ago
Ilimi

A kwanakin baya ne aka sanya hannu kan dokar bayar da bashin dalibai da kuma yadda aka ware kudi kimanin naira biliyan hamsin, a cikin kasafin kudin shekarar 2024, domin bayar da rancen dalibai. Duk da dai, manufofin da ke bayan kudirin na da kyau.

Kazalika, nazari ya tabbatar da cewa, manufar ba za ta haifar da da mai ido ba, yayin da kuma tunani da hasashe ya nuna rashin adalci da inganci da kuma mummunar manufa ga jin dadin daliban Nijeriya da sauran ‘dan kasa.

  • Sin Za Ta Dauki Matakan Da Suka Dace Kan Kamfani Da Wasu Mutanen Amurka Da Suka Shafi Batun Xinjiang
  • Kasar Sin Ta Ware Yuan Miliyan 400 Don Taimakawa Wadanda Bala’in Girgizar Kasa Ta Shafa A Gansu Da Qinghai

Sharuddan Bayar Da Bashin

Uku daga cikin sharuddan samun wannan rance na da matukar tsauri, wanda zai iya iyakancewa maimakon karfafa masu neman izini. Wadannan su ne na daya, mai garantin ma’aikacin gwamnati mai mataki na 12 ko kuma mutum mai daraja, yanzu mutum nawa ne ke da ma’aikaci mai daraja 12 a cikin danginsu ko kuma wani mutum mai daraja wanda kuma yake son daukar irin wannan nauyi?

Na biyu, dalibin da zai rattaba hannu a kan alkawarin biyan bashin a cikin wani kayyadadden lokaci, wa ke da tabbacin gobe idan aka yi la’akari da manufofin da gwamnati ke furtawa babu zato babu tsammani?

Na uku, dole ne dalibai su bi dukkanin wasu sharudan da hukumar lamuni ta dalibai za ta gindaya musu, wannan yana nuni ne da canza “dokokin bayar da bashin rana tsaka”. Kar a yi maganar cikas na ofisoshi da ke da alaka da kowane talafi na  gwamnati da yanayin siyasar Nijeriya.

Kalubalen Da Dalibai Da Iyaye Za Su Fuskanta

Duk da makudan kudaden da aka ware, matsalolin da za a fuskanta wajen samun wannan lamuni na da matukar yawa. Bugu da kari, ka’idojin da aka gindaya na nuna cewa, bashin na da  riba a cikinsa.

Damar Da Aka Rasa Da Manyan Tambayoyi

Biliyan hamsin(50) na da yawa, amma duk na rance ne ko kuma babban kaso ya shafi kayayyakin more rayuwa da suka shafi hukumar bayar da bashin ne? Hakan ya sa ayar tambaya a kan abubuwan da gwamnati ta sa a gaba. Idan manufar ita ce a taimaka wa dalibai don neman ilimi mai zurfi, me zai hana a ware wadannan kudade a matsayin  tallafi maimakon bashi?

Sakamakon Rashin Kishin Kasa

  1. Kamar yadda aka tsara a halin yanzu, rancen yana iya haifar da damuwa game da yiwuwarsa na habaka halin rashin kishin kasa a tsakanin matasa. Don haka, ya kamata gwamnati ta sanya hannun jari a harkar iliminsu a matsayin fifikon kasa, abin bakin ciki shi ne; gwamnati na fuskantar kasadar samar da tsarurraka masu daukar ilimi a matsayin mu’amala, maimakon hada hannun jari a makomar kasa.
  2. Aiwatar da kudirin rancen dalibai, wani lamari ne wanda ke nuni da rashin tausayawa daga bangaren jami’an gwamnati. Wadannan jami’ai, a lokacin karatunsu; sun ci gajiyar tallafin karatu kyauta tare da bayar da tallafin karatu da walwala iri daban-daban. Bambance-bambancen da ke tsakanin abubuwan da suka samu da kuma kalubalen da ke tattare da kudirin rancen daliban; ya sanya ayar tambaya a kan yadda gwamnati ke kokarin kyautata rayuwar al’ummarta.

III. Raba kudade a matsayin rancen dalibai ya bambanta sosai da abubuwan da aka ware a wasu wurare cikin kasafin kudi. Makudan kudaden da aka ware domin sayen Jif-jif, gina wa mataimakin shugaban kasa gida na nuna rashin fifiko da bai dace da ka’idojin mulki ba.

Mu Kwatanta Alfanun Bashi Da Sikolashif Mu Gani:

  1. Rashin Daidaito:
  • Lamunin dalibai zai haifar da cikas ga dalibai masu fama da matsalar tattalin arziki.
  • Sikolashif/tallafin dalibai na makaranta na magance rarrabuwar kawuna ta hanyar bayar da taimakon kudi ba tare da nauyin biyan bashi ba. Wannan yana tabbatar da cewa duk dalibi, ba tare da la’akari da yanayin tattalin arzikinsa ba, na da damar samun ingantaccen ilimi. (Shin wannan bai kamata ya zama ma’auni mafi dacewa ba?)
  1. Ingantaccen Amfani Da Albarkatu:
  • Tsarin lamuni na dalibi, na bukatar ingantaccen kayan aikin gudanarwa, gami da kirkirar hanyoyin bayar da lamuni, bin diddigi da tarawa. Wannan aikin gudanarwa; tabbas zai karkatar da albarkatu daga burin farko na tallafa wa ilimi.
  • Sikolashif ya fi daidaitawa ta fuskar gudanarwa. Kudaden na tafiya ne kai tsaye ga dalibai tare da rage sarkakkiya a tsarin mulki da tabbatar da ingantaccen rabon albarkatu, don neman ilimi.
  1. Karfafa Tattalin Arziki Da Ci Gaban Kasa:
  • Lamunin dalibai zai kawo tsaiko wajen bayar da gudunmawar tattalin arzikin da ‘ƴan kasa masu ilimi za su bayar, don ci gaban kasa domin abin damuwa zai fi yadda za a biya ko kuma kaucewa biyan kudin.
  • Sikolashif/tallafi, wadanda suka kammala karatunsu ba tare da bashi ba sun fi bayar da gudummawa ga ci gaban tattalin arziki ta hanyar kasuwanci, kirkire-kirkire tare da sanya hannun jari a kan lokaci cikin al’ummominsu.

Ina  Mafita?

  1. Gabatar da guraben karo karatu mai inganci, domin kwadaitar da nagartar ilimi, domin zaburar da dalibai su himmatu wajen kara kwazo tare da bayar da gudumawa ga al’umma.
  2. Kara yawan kasafin kudi ga Ilimi tare da karkatar da wani bangare nasa zuwa guraben karo karatu, tallafi da kuma inganta ayyukan ilimi baki-daya.

III.     Hadin gwiwar gwamnati da kanfanoni masu zaman kansu, domin habaka kokarin gwamnatin ta hanyar gabatar da sabbin nau’ikan tallafin kudi.

A karshe:

A cewar Nelson Mandela, “Ilimi shi ne makami mafi karfi, wanda zaka iya amfani da shi don canza duniya baki-daya.”Mu yi amfani da wannan makami cikin hikima da adalci, domin ci gaban al’ummar Nijeriya.

Alhaji Adamu Rabiu ya rubuto daga Kaduna.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Raya Al’ada: Bikin Kalankuwa Na 2025 A Kano
Bakon Marubuci

Raya Al’ada: Bikin Kalankuwa Na 2025 A Kano

October 3, 2025
Me Ake Nufi Da Ado? 
Bakon Marubuci

Me Ake Nufi Da Ado? 

September 26, 2025
Ranar Hausa: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka
Bakon Marubuci

Ranar Hausa: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

August 30, 2025
Next Post
Manzancin Annabi (SAW) Da Yadda Allah Ya Yalwata Kirjinsa

Manzancin Annabi (SAW) Da Yadda Allah Ya Yalwata Kirjinsa

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version