Daga Abubakar Abba
Gwamnatin Tarayya ta fara shiye- shiryen rufe hukumar sake farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa (NERFUND) saboda kasa gudanar da wani abin a zo a gani da kasa samar da bashi na sama da Naira biliyan 17.5 .
Wata majiya a ma’aikatar kuɗi ta ƙasa ta sheda wa kafar Dillancin Labarai (NAN) hakan a Abuja, inda majiyar ta ce, tuni an kafa kwamiti don rufe gidauniyar a ƙarshen watan Okutobar wannan shekarar.
Majiyar ta ci gaba da cewa, ana sa ran kwamitin zai gabatar da shawarwari don duba haƙoƙkin ma’aikatan gidauniyar da kuma abin da za a yi da kayayyakin aikin da ke ofishin na hukumar. Bugu da ƙari kwamitin zai ba da shawarwari ga hukumar da za ta ci gaba da shari’un da ke gaban Kotu da hukumar ta shigar don dawo da biliyoyin kuɗin da aka ba da bashin su amma ba a dawo da su ba.
Majiyar ta bayyna cewa, an ba da basussukan ne ga waɗanda suka karɓa ba tare da sun kawo masu tsaya masu ba, inda hakan ya janyo basussukan suka hau fiye da yadda ake zato.
A wata sabuwa kuma, wani ma’aikaci a hukumar da bai son a ambaci sunansa ya bayyan cewar, tuni an gaya wa ma’aikatan dage Gidauniyar a kan shirin rufe ofishin.
Ya ce, “An ba mu zaɓi na ko mu yi ritaya ko ko a sallame mu daga aiki, kuma Manajin Darakta ya sheda mana cewar, mahukuntan hukumar suna gudanar da aiki da Babban Sakatare na ma’akatar kuɗi ta tarayya a kan maganar.” Ya ci gaba da cewa, “sun yi mana alƙawarin ba za mu rasa ayyukanmu ba za su yi mana canjin aiki zauwa wata ma’akata.
An ƙirƙiro da hukumarce, a ƙarƙashin Doka ta biyu ta shekarar 1989 don samar da hanyoyin bunƙasa ayyyukan matsakaitan sana’o’i ta hanayar ba da bashin kuɗin tallafi na Naira miliyan 300. A shekarar 2002, Gwamnatin Tarayya ta haɗe Bankin Masana’antu (NIDB) da Bankin Kasuwanci (NBCI) da Masana’antu, inda ya koma Bankin Masanatu (BOI). Sai dai Gwamnatin ta ware cibiyar ta (NERFUND) daga cikin cibiyoyin kuɗi na ƙasa.
Bugu da ƙari cibiyar tun da farko kuɗin ta ya haura biliyoyin Naira, amma sakamakon rashin iya gudanar da aiki, cibiyar ta durƙushe a farkon shekarar 2013, inda hakan ya janyo kasa gudanar da ayuukan da aka ɗora wa cibiyar alhakkin gudanarwa. A cikin watan Yunin shekarar 2016, ma’aikatan hukumar sun gudanar da zanga-zanga a kan alumbazzaranci da ake yi da kuɗin hukumar.
Gwamnatin Tarayya ta hanyar Ministan Kuɗi Kemi Adeosun ta kawo ɗauki ta hanayar ɗaukar mataki na farko na rufe hukumar saboda kasa daidaita tsakaianin mahukuntan hukumar da ma’aikatanta don kauce wa taka doka. Bayan sati biyu kuma, Ministan ta umarci ma’aikatan da su koma kan aikinsu, sannan kuma ta naɗa Dakta Ezekiel Oseni a cikin watan Agusta a matsayin Manajin Darakta hukumar na riko.
Sai dai, a cikin shekara ɗaya da naɗa Dakta Ezekiel Oseni sai kuma gwamnati ta amnince da a rufe hukumar.