Bashin NIRSAL: Anya Talaka Na Da Rabo A Ciki Kuwa?

NIRSAL

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta samar da wani tsari na bayar da bashi ga al’ummar kasar masu sana’o’i daban-daban a karkashin kulawar Babban Bankin Nijeriya (CBN), wanda shi kuma ya dora alhakin tafiyar da lamarin kan bankinsa na kula da kananan sana’o’i da matsakaita, wato Bankin NIRSAL.

Hakan ya biyo bayan halin da tattalin arziki jama’a ya tsinci kansa a ciki ne na matsin lamba da zaizayewa tun bayan bullar Annobar Cutar Korona, wacce ta yi kaca-kaca da aljihun talakawan kasar.

Samar da wannan tsari abin maraba ne matuka da gaske, idan a ka yi la’akari da karancin kudin ruwa da bashin ya ke da shi, wanda bai wuce kashi biyar cikin 100 ba da za a caji duk wanda ya amshi bashin, sabanin kudin ruwan da bankunan kasuwanci su ke cajar abokan huldarsu na kashi 25 zuwa 30.

Dadin dadawa, gabanin bullar Annobar Korona bankin NIRSAL ya na bayar da bashi ne da kudin ruwa na kashi tara kawai, amma duk da haka Gwamnatin Nijeriya ta ce, a rage shi zuwa kashi biyar har zuwa lokacin da al’amura za su lafa kan annobar. Wannan ma abin a yaba ne.

To, sai dai kuma tun bayan bayyana samun waccan dama, daga dukkan alamu ainihin talakan kasar mai gudanar da sana’o’i, musamman a matsayi na matsakaitan sana’o’i, ba ya iya samun wannan damar.

Binciken da LEADERSHIP A YAU ta gudanar a tsakanin akasarin al’ummar kasar ya nuna cewa, mafi yawan mutanen da su ka cancanci samun bashin ba su same shi ba, duk da cewa, su na so ko kuma ma a ce sun nemi bashin, amma shiru ka ke ji, kamar malam ya ci shirwa.

Shin mene ne ya janyo wannan matsalar? Binciken da mu ka gudanar ya nuna cewa, akwai dalilai da dama kan faruwar hakan, wadanda su ka hada da ka’idojin da a ka gindaya na samun bashin, wadanda su ka hada da amfani da intanet wajen neman bashin, wanda akasarin masu bukatar wannan bashi ba su da zurfin ilimi ko kuma kwarewa ta iya neman wannan bashi ta hanyar intanet.

Wannan ya bai wa masu damfara damar bibiyar jama’a su na damfarar su da sunan za su taimaka mu su wajen samar da rancen.

Ba nan kadai ba, su kansu wadanda su ke da ilimin da zai iya ba su damar samun rancen, su na fuskantar matsaloli daban-daban, wadanda su ka hada da tsare-tsare da fi’ilin bayar da bayanai da a ke bukata daga gare su. Bankin CBN ko kuma mu ce Bankin NIRSAL sun manta da cewa, mafi yawan sana’o’in ba su da cikakken tsari dauwamamme, illa dai akwai akwai sana’ar ko kasuwanci.

Misali a nan shi ne, a cikin ka’idojin da mai neman bashin zai cika, akwai bayar da bayanin asusun banki (account statement) wanda su ke gudanar da ksuwancin sana’ar na tsawon shekaru uku cur! Hakika wannan ka’ida ta na da wahalar cikewa ga masu kananan sana’o’i, musamman ma a yankin Arewa. A fili ta ke cewa, ba kowa ke yi wa sana’arsa asusun banki ba.

Haka nan akwai tambayoyi da dama wadanda su ke da wuyar amsawa ga mai karamar sana’a, musamman ta fuskar yadda tsarin nasu na intanet ya ke bayar da kididdiga da lissafin bayanan kudade, faduwa da kuma riba ta fuskar tasarrufi.

Bayan nan kuma, bankin na NIRSAL ba ya sanar da masu neman bashin matsayinsu matukar ba su cancanci amsar bashin ba (wanda abinda ke faruwa kenan ga akasarinsu). Su kan mance da mutum ba tare da sun sanar da shi cewa, an amince ko akasin hakan ba, wanda hakan ya na sanya wa mutum ya cigaba da zaman jira har sana’arsa ko kasuwancinsa ya samu matsala, saboda igiyar zato na jan sa. A nan yakamata duk wanda ya nemi rancen a sanar da shi matsayinsa da zarar an yanke hukunci kan hakan, don ya fuskanci abinda ya dace.

Da yawan masu neman bashin su kan kasa aiwatar da wasu abubuwan bisa tsammanin kada su tsunduma wani abin daban, sai kuma daga bisani rancen ya fito.

Kazalika, tsawon lokacin da a ke dauka kafin a gama duba neman bashin da mutane su ka yi ya na yin tsawo da yawa ta yadda har ma sana’o’in su na iya rushewa, saboda jinkiri da a ka samu. A nan yakamata gwamnati ta sani cewa, tafiyar hawainiyar da lamarin ya ke yi ya saba da ikirarin gwamnatin na bayar da tallafi, don farfado da halin da a ka tsinci kai sakamakon bullar annobar Korona.

Muhimmin abu dai shi ne, ya wajaba, idan har gwamnati da gaske ta ke yi cewa, ta shirya bayar da bashin ne da sunan taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin masu sana’o’i, to a saukaka hanyoyin neman bashin da kuma rangwanta cika ka’idoji. Idan kuma ba haka ba, to mafi yawan talakawan kasar ba za su san a na yi ba.

Exit mobile version