Connect with us

RIGAR 'YANCI

Bata-gari: Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano Ya Ciri Tuta – Sarkin Rano

Published

on

An yabawa wa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano Habu Ahmadu Sani bisa kokarin da ya ke na Samar da tsaro a Jihar Kano da kuma yankunan masarautun Jihar Kano guda biyar. Mai martaba Sarkin Rano Alh Kabiru Mohammad Inuwa ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke mika lambar yabo ga Kwamishinan yan sandan a Kano.

A cewar Sarkin, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano ya bada gagarumar gudunmmawa wajen Samar da cikakken tsaro da kyakkyawan yanayi a Masarautar Rano. Ta hanyar kakkabe bata gari da suka addabi yankin. Ya kuma ce masarautar Rano a shirye take wajen aiki da jami’an ‘Yan Sanda ta hanyar basu cikken goyon baya akan aikin su na tabbatar da tsaro dari bisa dari. Inji Sarkin.

Daga anan Sarkin sai ya yi Kira ga wadanda aka rantsar da su rika taimaka wa jami’an ‘Yan Sanda kan yin aiki tsakaninsu da Allah da kuma bada hadin kai wajen Samar da tsaro da kawar da batagari a fadin Jihar Kano.

Shi ma a nasa Jawabin Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano CP Habu Ahmadu Sani wanda ya rantsar da masu taimakawa ‘Yan sanda a fannin tsaro na cikin al’umma cewa ya yi rundunar ‘Yan Sanda ta samu nasarori da dama da taimakon ‘Yan Sandan cikin Al’umma. (Community Policing).

Kwamishinan ‘Yan Sandan ya kuma bayyana cewa rundunar tayi nasarar cafke wasu batagari a lokacin da annobar Korona ta barke, inda rundunar tayi nasarar cafke wadanda ake zargi da fashi da makami su 18, da kuma guda bakwai masu garkuwa da mutane, sai wadanda ake zargin da Zamba cikin aminci su 10, ya yinda rundunar ‘Yan Sandan tayi nasarar cafke Mutane 14 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, da ‘Yan daba su 317 wadanda aka kama su a wurare daban daban da muggan makamai da harsashi 1,289, an kuma kama su da motoci 4, babura masu kafa uku da sauran miyagun kwayoyi.

Kwamishinan ya bayyana cewa dukkan wannan nasarori an samu ne da gudunmmawa al’umma ta hanyar ba su hadin kai da kuma bayyana maboyar batagarin.




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: