Batan Janar Alkali: An Binne Gwarshi A Asirce -Hukumar Sojin Nijeriya

Manjo-Janar Benson Akinroluyo ya yi zargin an binne gawar Manjo-Janar Alkali Idris da ya bace a kan hanyar shi ta zuwa Bauchi daga Abuja, a asirce, inda yake zargin wasu daga cikin al’ummar garin Dura Du ne suka binne shi a wani fili da har yanzu ba a kai ga gano filin ba.

A farko an binne shi ne a wani rami da bashi da zurfi, amma lokacin da jami’an soji suka matsa da bincike, sai aka tone shi daga ramin, inda ake tsammanin sun sake tona wani ramin na daban, don sake binne shi.

Akinroluyo ya shaida wa manema labarai wannan bayanin ne yau Juma’a a garin Jos, a yayin da yake ganawa da manema labarai.

‘Bincika ya nuna mana, lokacin da muka matsa kaimin bincike, bayan mun gano motar Janar Alkali, sai wasu daga cikin al’ummar garin Dura Du suka hada tawagar mutum 10, don tone gawar Manjo-Janar din daga ramin da suka binne shi a farko, zuwa ga wani sabon rami wanda yafi wancan zurfi, sannan sun yi hakan ne a cikin sirri.’ inji Akinroluyo

Al’ummar kauyen ta ji tsoron abinda zai faru in muka gano gawar Manjo-Janar din, don haka sai suka yanke shawarar tone shi daga wancan ramin na farko, inda suka yi wani ramin a asirce, sannan suka nada tawagar mutum 10 wadanda zasu yi aikin birni shi a sabon ramin na sirri, mun samu wani mutum, wanda ya kware a aikin taskace gawa, shine ya bamu wannan bayanin, yace an dauke shi don yin aikin tone gawar daga ramin farko zuwa wani ramin na asiri.

Jami’an sojin sun kama mutane hudu da dukkansu suka nuna musu wannan ramin na farko wanda bashi da zurfi, a matsayin ramin da aka binne gawar Manjo-Janar Alkali din, amma dai alamu sun nuna an tone ramin, an kuma cire gawar.

Bayan motar Janar Alkali, akwai wasu motoci da aka samu a wannan kududdufin da aka samu motar Janar Alkali, akwai mota kirar bas, wacce ta bace tun a cikin watan Yunin 2018, sannan akwai wata jar mota kirar Rover wacce ita kuma ta bace da mutanen cikinta tun a shekarar 2013.

Zuwa yanzu jami’an tsaro suna neman wasu mutane ruwa a jallo, mutanen sune kamar haka, Chuwang Samuel, Nyam Sam, Pam Dung, Mathew Wrang, Moses Gyang da Timothy Chuan, sai wasu da ake zargin suna da masani kan batar Janar din, mai unguwar Dura Mista Yakubu Rap, da wani Chuwang Stephen.

Exit mobile version