Abdullahi Muhammad Sheka" />

Batun Bayar Da Ilimi Kyauta: Sarkin Kano Ya Bukaci Sauran Gwamnoni Su Yi Koyi Da Ganduje

A cigaba da kokarin da Gwamnan Jihar Kano ke yi na bayar da ilimi kyauta kuma wajibi ga dukkanin dan asalin Jihar Kano, Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bukaci sauran Gwamnonin Nijeriya su yi koyi da Gwamna Ganduje domin tabbatar da mutuntaka tare da sauran hanyoyin samun ingantaccen cigaba.

Da fari dai Sarkin na Kano, ya taya Gwamna Ganduje murnar wannan kyakkyawan tunani wanda ya bayyana shi da cewa, abu ne mai matukar amfani domin samun ingantacciyaral’umma a nan  gaba, “ko shakka babu ina da kyakkyawan yakinin cewa, wannan tunani ya biyo bayan niyyar hidimta wa al’ummar Jihar Kano ne baki-daya.”

Kazalika, Mai Martabar ya bayyana wannan jinjina tasa ne a lokacin da Gwamnan ya karbi bakunci Wakilai daga Bankin Zenith, wanda Dakta Sani Yahaya ya jagoranta bisa wakiltar Manajan Darkata na Bankin. Haka nan, wannan wakilci ya jinjinawa Gwamna Ganduje bisa samun nasarar da ya yi a Kotun sauraron korafe-korafen zabe tare da yin alkawarin hada hannu da Gwamnatin Kano domin aiwatar da shirin ilimi kyauta kuma wajibi ga duk dan asalin wannan jiha.

Haka zalika, Sarkin ya jaddada cewa, “wannan shi ne zahirin abinda kasa ke bukata, domin kuwa kowace irin kasa na bukatar tabbatar da kyakkywar kulawa tare da jajircewa domin samun cikakkiyar nasara, musamman kasancewar ilimi shi ne kashin bayan cigaban kowace irin al’umma”, in ji Mai Martaba.

Har ila yau, a cewar Sarkin na Kano abinda mai girma gwamna ke yi wani kyakkyawan misali ne kuma ingantacce wanda ake aiwatar da shi domin biyan bukatun cigaban al’umma. Sannan sai ya ja hankalin sauran jihohin kasar nan tare da nuna musu muhimmancin koyi da irin wannan kyakkyawar aniya ta Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

“Yana da muhimmancin gaske ga kowa da kowa domin hada hannu tare da kuma bayar da gudunmawarsa domin samun nasarar wannan kyakkyawan cigaba a Jihar Kano da ma kasa baki-daya”, in ji shi.

Daga nan ne kuma, sai ya sake yin kira ga gwamnati tare da sauran masu ruwa da tsaki da cewa, wajibi ne su hada hannu guri guda domin taimakawa dimbin al’ummarmu da kuma tabbatar da ganin cewa ba su zama marasa amfani ba. Kazalika, Sarki Sanusi ya bayyana goyon bayansa da cewa, “kamar yadda Gwamna ya nuna aniyarsa ta cigaban al’ummarmu, to fa wajibi ne ita ma al’ummar tamu ta sauya zuwa wata muhimmiyar kadara wadda za ta amfani sauran al’umma bakidaya.”

Da yake maida nasa jawabin ga Wakilan Bankin na Zenith, Gwamna Ganduje ya sake jaddada cewa, babu wata gajeruwar hanyar samar ingantaccen ilimi, don haka wajibi ne sai mun tashi tsaye domin inganta shi”, a cewar gwamnan.

Haka zalika, shi ma Wakilin tawagar Bankin na Zenith, Dakta Yahaya bayan gabatar da sakon taya murna ga Gwamna Ganduje, ya tabbatarwa da gwamnan cewa, “Bankin Zenith na tare da gwamna dari bisa dari akan batun shirinsa na bayar da ilimi kyauta kuma wajibi ga kowa tun daga matakin Firamare har zuwa Sakandire. Sannan batun shigar da tsarin karatun Almajirai a wannan Jiha ta Kano, shi ma wani muhimmin cigaba ne wanda a nan gaba tarihi ba zai taba mantawa da gwamnan ba, don haka muna yin alfahari da kai mai girma gwamna”, in ji shi.

Wakazalika, wannan Banki a koda-yaushe a shirye yake domin hada hannu da Gwamnatin Jihar Kano, domin ciyar da harkokin ilimi gaba. “Wadannan wasu littattafai ne wadanda za a yi amfani da su a makarantun Firamar da na Sakandire.” Kamar yadda Babban Darkatan Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya shaida wa Jaridar Leadership A Yau Asabar.

Exit mobile version