Batun Katin Chrestmeti Tamkar Wasan Kwaikwayo Ne Mai Ban Dariya Da Kasashen Yamma Suka Gabatar

Kwanan baya, jaridar “The Sunday Times” ta Birtaniya, ta ba da wani labari na zargin kasar Sin da cewa, gidan kurkuku ta dake Qingpu na birnin Shanghai, na tilastawa fursunoni ’yan ketare yin aikin kwadago, har ma kafofin yada labarai na kasashen yamma, sun yada wannan labarai ba iyaka. Amma, ’yan kafar CMG dake Birtaniya, sun gano wasu matsala a cikin labarin.

Yan kafar sun ce da farko dai, an bada labarin ba bisa gaskiya ba. Kuma jaridar “The Sunday Times” ba ta yi bincike kan lamarin ba, kawai dai ta gabatar da labari mai taken “Katin Tesco: Fursunan gidan kurkuku a kasar Sin su ne suka samar da su”, don zargin kasar Sin cewa: Ta mai da wadannan fursunoni bayi.

Na biyu, jaridar ba ta ba da labari bisa adalci da daidaito ba. Wato dai an ba da labari ba tare da zantawa da wata hukuma, ko mutum na kasar Sin ba. Ban da wannan kuma, sun yi biris da takardar shaidu da Tesco ya bayar, bisa sakamakon nazarin da wata hukumar bincike ta nuna, cewa, babu shaidu dake bayyana cewa, kamfanin Sin ya keta ka’idar hana amfani da kwadago kan ’yan fursuna. Kaza lika labarin ya yi karyar cewa, Tesco ya daina gudanar da hadin kai da kamfanin kasar Sin. Na uku, hana bunkasuwar kasar Sin, wani mataki da wasu mutane, ko hukumomin kasashen yamma suka dade suna dauka, don neman samun moriya ta kudi ko siyasa.

An ce, a watan Yuli na shekarar 2013, gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar cin kamfanin GSK, wato kamfani mafi karfi ta fuskar samar da magunguna a duniya tara, wadda yawanta ya kai RMB yuan biliyan 3, kwantankwacin dalar Amurka miliyan 461. Sakamakon hakan, kamfanin ya yi hayar Peter Humphrey, mai aikin bincike mai zaman kansa a wancan lokaci, don ya yi bincike kan wasu ma’aikatan dake karbar rashawa. Yayin da yake gudanar da aikin bincike, ya gano bayanan daidaikun mutane ba bisa dokar kasar Sin ba, sakamakon haka, an tsare shi cikin gidan kurkuku na Qingpu. Abin mamaki shi ne, Humphrey bai ji kunya kan lamarin ba, har ma ya rika kai hari kan kasar Sin, kan abubuwa da dama dake shafar kasar bisa wannan batu, matakin da ya samar masa dimbin kudade. (Amin[tps_header][/tps_header][tps_title][/tps_title]a Xu)

Exit mobile version