Batun Kirkira Ko Raja’a A Bangaren Sana’a Guda

Sana'a

Tsokacin yau zai yi duba ne game da abinda ya shafi sana’a musamman yadda wasu mutanen ke tattara a kan sana’a guda daya, sabanin kirkirar wata sana’ar ta daban wadda ba ta yi yawa ba. Kirkirar sana’a babba ko karama na kara bude hanyar samun wasu sana’o’in tare da bunkasa al’amuran rayuwa, da saukakewar wasu abubuwan, da kuma ci gaban al’umma baki daya, da dai sauransu. Wannan shafi ya ji ta bakin wasu matasan game da yadda matasa za su samar da sabbin sana’o’i da kuma dalilin da ya sa mutane suke raja’a akan sana’a guda daya, tare da tunanin samar da sana’ar da ta dace. Ga dai bayanan nasu kamar haka:

 

Maryam Alhassan Dan’iya (Maryam Obam):

Matasa za su iya samar da sabbin sana’o’i da yawa idan suka cire girman kai, mafi yawan matasa suna raja’a akan sana’a guda daya ne idan sun ga abokin su ya na yi kuma suka ga yana samu sai suma su ce bari su yi irinta mai makon suma su fito da irin tasu ta daban ta yadda za su bambanta sana’a, ina ga a tattara akan sana’a guda daya ba shi da amfani misali yanzu idan wancan ya fara nasa kaima ka fara naka daban sai kuga har taimakon juna ake amma idan ana sana’a iri daya sai kiga kyashi da hassada ya shiga. Akwai sana’o’i da dama misali kamar siye da sayarwa, idan ka ga mutum na sana’a za ka iya dorawa akan ‘social media’ kayi tallah in ana so sai ka kara taka ribar akai, in mutum ya siya kaga ka tallatawa mutum kaima ka samu riba wannan ina ganin ita ce babbar hanya musamman wadanda ba su da jari na sana’a. Za’a iya bunkasa sana’a ta hanyar saida abu mai inganci, rike alkawari tsakanin mai saidawa da masu siye, sannan ka tabbata kana da jari baka taba kudin sana’ar ta yadda duk sanda aka bukaci abinka za a samu, ba wai in an zo ace babu ba, ka cinye kudin jarin hakan na ruguza sana’a duk karbuwarta.

 

Aisha Musa Yankara:

Matasa za su rinka tunanin samo sana’a ta hanyar amfani da kwakwalwarsu da Iliminsu da tunaninsu. Yawan kwaikwayon sana’a bai da amfani gaskiya ya kamata ace matasa muna karkata hankulanmu akan kashe karshen sana’o’i, hausawa sunce “Zama waje daya tsautsayi”. kasuwanci ma zai taimakawa al’umma sosai, ta hanyar kyautawa da kuma tsayawa ka yi domin Allah, Sana’a tana da dad’i sosai dan haka mu kara dagewa wajen ganin mun rike kanmu da iyalanmu ta hanyar da ya da ce Domin rashin sana’a shi ke kawo da yawan wannan ta addancin.

 

  1. Shuraim Ibadan:

Akwai hanyoyi da dama da matasa za su bi dan samar da sabbin sana’o’i kamar ta yanar yanar gizo da noma da sauransu,

Raja’a kan sana’a daya gaskiya ba shi da amfani yana da kyau matasa su runka canja sana’a kamar kananan sana’o’i da suke rainawa idan sun yi la’akari da karami ake zama babba,

Noma yana da matukar amfani ga al’umma, kuma idan al’umma za su riketa tabbas za su ji dadi. Ta hanyar kokarin fito da abubuwan da aka san al’umma na bukata da rashin tsawwalawa ma’ana a sauke farashin dai-dai da yadda al’umma za su iya siya.

 

Dr. Maryam Sokoto:

Hanya mafi sauki da matasa za su samar da sababbin sana’o’i ita ce, sanin ciwon kai! Matuka matasa suka san ciwon kawunan su to tabbas samar da sababbin sana’o’i karamin abu ne. Tom gaskiya idan har ki ka ga matasa sun tattara a kan sana’a daya hakan yana da alaka ne da ra’ayin kawunan su! Gaskiya hakan ba shi da amfani ko daya!. Sana’o’i ga sunan da yawan gaske, sana’a daya da za ta taimaki al’umma ita ce mutum ya yi amfani da karfin jikinsa ya nemi sana’a wacce ya ke hangen za ta amfane shi da shi da iyalinsa har ma wani ya ci amfaninta. Haryar da za a bi domin bunkasa sana’a ita ce dai talli tal! Matasanmu su san ciwon kawunansu su tsaya kan kafafuwansu, ka da su dogara da sana’a daya, yi wannan kama waccan adai yi ta yi domin bunkasa sana’a. Shawarata ga masu yin sana’a ita ce, su ji tsoron Allah a dukkanin lamurransu, su rike gaskiya da gasgatawa, fatan Ubangiji Allah ya ba su dukkanin abinda su ke nema da zufan jikinsu na alkhairi.

 

Aisha Idris Abdullahi (Aleeshat):

Ta hangar dogaro da kai da kuma amfani da hankali da tunani, Wasu suna duba da wane sana’a ka za yake daga farawarsa gashi har ya yi kudi dan haka muma wanan sana’ar zamu fara basa duba da cewa su mutum duk idan arzikinsa yake yana zuwa ya tadda shi ba gaskiya tattarewa ga sana’a daya sam! bai da amfani saboda samar da sana’a da yawa zai sa saura matasa marasa aikin yi su samu sana’a. Noma zai taimaka wa matasa sosai idan nace noma ba wai Noman damuna nake nufi ba kamar su Noman shinkafa alkama ridi shima babbar sana’a ce wanda duk wanda ya yi shi dole sai wasu da dama sun samu aikin yi ta karkashin sa, Hanyoyi da dama musamman da zamani ya zo mana da ‘social media’ zamu iya bunkasa sana’ar mu ta hanyar tallata ko wace irin hajar mu a ‘social media’. Sharawata gare mu matasa shi ne mu tashi mu dage ba maraya sai rago ba kuma na kasheshe sai kasheshe dan haka mu mike mu kara zage dantse Allah ya bamu sa’a.

 

Nazifi Yarima (N. Yareema) Jihar Kano:

Na farko Neman ilmin kasuwancin kafin a fara shi. sai kuma Samar da jarin da za a yi kasuwancin sune hanyar farkon ta samun damar Samar da sabbin sana’o’i. Eh ta wani fannin mutanan mu sun raja’a ne akan sana’a daya saboda wasu karancin jari ne, wasu kuma sun raja’a, akan hakan da ginuwa akan hakan tun farko za ka ga mutum Irin direba ne shi ko tela ne shi zai yi wuya kaga ya canza sana’a. Sana’o’i da yawa mana, kamar saida ‘pure water’, Turin baro. Ga mata kuma Dinki

Ko kitso ko lalle da kunshi. Na farko fadada tunani akanta sana’ar kullum ka dinga kokarin zamanartar da ita, yin adashin gata da rage almubazarranci da kudi da sayen abubuwan da basu zama dole ga mutum ba. Ta wannan hanyar indai an bi insha Allahu za a bunkasa kasuwa. shawara ta farko kafin ka fara sana’a ka nemi iliminta, na biyu kullum ka dinga fadada tunaninka akan kasuwarka, sannan kullum ka rinka lissafin riba kake samu ko faduwa kake yi, wanne ci gaba kake samu, sannan ka rinka adana wasu kudin ‘personal’ saboda tunanin mai zai je ya zo nan gaba.

 

Jabeer M. Hassan (Jaheed):

Yana daga cikin abinda yake jawo rashin abin yi, abin dogaro ko sana’a ga matasa shi ne raina sana’a, musamman aikin hannu, matasanmu da yawa suna son jin dadin rayuwa amma kuma suna son jin dadin ya same su ne cikin sauki ba tare da sun wahala sosai ba. Daga cikin hanyoyin magance zaman banza ga matasa shi ne kawai dogaro da kai, matasa su nemi sana’ar hannu, tunda akwai abinda mutum zai iya koyo, kamar kafinta, dinki da sauransu. A wannan lokaci da ake ciki na tsadar rayuwa da babu har a sami wanda zai ce zai raina sana’a? Idan mutum yanada irin wannan tunani na raina karamar sana’a gara ya daina, don bai san ta inda Allah zai fidda arzikinsa ba, ta yiwu watarana sana’ar ta zama babba. A wannan lokaci da ake ciki ya kamata gwamnati ta taimakawa matasa musamman masu dogaro da kai, ta haka nake ganin za a dan ji dama-dama, kuma radadin talaucin da ke addabar mutane zai rage, da yawan matsannan masu ‘yar karamar sana’a suna bukatar taimako don tallafawa kasuwancin su.

 

Sadiya M. Kabeer Jihar Kano:

A gaskiya bai kamata ace mutum yana sana’a daga an ga ta karbe shi sai kowa ya ce ita zai yi sai kaga an kashe  sana’ar, saboda da ‘yan gasa, sun hadu sun kashe sana’ar, wannan bai kamata ba kama ya yi kowa ya kirkiri tashi ya gwada sai ya ga Allah ya taimake shi wannan shi ne shawarata.

Exit mobile version