Batun Mika ‘Yan Gudun Hijira Ya Nuna Halayyar Kasashen Yamma
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Batun Mika ‘Yan Gudun Hijira Ya Nuna Halayyar Kasashen Yamma

byCMG Hausa
3 years ago
Hijira

‘Yan gudun hijira mutane ne mafi fama da mawuyacin hali a duniya. Idan dai akwai dama, to, ba za su yi watsi da gidajensu, da barin iyalai, har su fita zuwa wata kasa ta daban ba, inda suke jure zaman rayuwa cike da wahalhalu. Sai dai yanzu har ana kara wulakanta su: Kasar da suke kaura cikinta ka iya tusa keyarsu zuwa wani wuri mai nisa, inda ba su taba tunani ko tsammanin zuwa ba.

A ranar 14 ga wata, kotun kare hakkin dan Adam ta nahiyar Turai ta hana tashin wani jirgin sama mai daukar nauyin jigilar ‘yan gudun hijira daga kasar Birtaniya zuwa Rwanda.

  • Xi Ya Yi Kira A Hada Gwiwa Don Yaki Da Rashawa

Kafin afkuwar lamarin, kasar Birtaniya da Rwanda sun kulla wata yarjejeniya, inda aka daddale cewa, Birtaniya zata biya kudi fam miliyan 120 ga Rwanda, don kasar Rwandan ta karbi ‘yan gudun hijira da suka yi satar ketarawa zuwa kasar Birtaniya. Ko da yake, ba a fara gudanar da yarjejeniyar ba tukuna, sakamakon kin amincewar da bangarorin kasa da kasa suka nuna, ciki har da hukumar ‘yan gudun hijira ta MDD suka nuna. Amma gwamnatin kasar Birtaniya tana ci gaba da neman aiwatar da yarjejeniyar.

Me ya sa ake kin amincewa da matakin da kasar Birtaniya ta dauka?
Saboda da farko dai, kasar Birtaniya, da Amurka, da sauran kasashen yammacin duniya, laifinsu ne yadda suka haddasa matsalar samun tarin ‘yan gudun hijira a duniya. Wadannan kasashe sun kaddamar da yake-yake a kasashen Iraki, da Afghanistan, da tsoma baki tare da tsananta yanayin rikici a Syria, da Libya, da Venezuela, da dai sauransu.

Hijira

Irin matakan da suka dauka sune ainihin dalilan da suka haddasa karuwar ‘yan gudun hijira a duniya. Saboda haka ya kamata kasashen yamma su dauki nauyin kula da ‘yan gudun hijira, maimakon a tusa keyarsu zuwa wata kasar dake nahiyar Afirka.

Ban da wannan kuma, matakin kasar Birtaniya ya nuna wani yanayi na rashin adalci, inda matukar akwai kudi, to, ana iya yin kome. Su kasashe masu sukuni, sai su biya kudi, sa’an nan za su iya magance daukar nauyin kulawa da ‘yan gudun hijira.

Ganin haka zai sa su ta da rikici, da lalata yanayin zaman rayuwar jama’ar sauran kasashe, ba tare da wata damuwa ba. Idan an samu ‘yan gudun hijira, sai a tusa keyarsu zuwa kasashe masu tasowa, ba tare da tsoron samun wani tasiri daga lamarin ba.

Sa’an nan lamarin ya nuna halayyar kasashen yamma a fannin hakkin dan Adam. Da ma kasashen suna kallon kansu a matsayin “Masu kare hakkin dan Adam a duniya”, har ma su kan tsoma baki a harkokin cikin gida na sauran kasashe.

Sai dai ko da gaske ne suna kare hakkin dan Adam a duniya? Idan mun dauki kasashen Amurka da Birtaniya a matsayin misali. Kasar Amurka ta yi ta kaddamar da yake-yake a kasashe da dama, inda take kisan mutanen kasashen, da aiwatar da mulkin danniya a duniya. Yayin da a nata bangare, kasar Birtaniya tana kallon ‘yan gudun hijira a matsayin kayayyaki, tana neman mika su ga sauran kasashe ba tare da kulawa da yanayin da wadannan mutane suke ciki ba.

Ta wadannan batutuwa, za mu iya ganin cewa, kasashen yamma kullum suna neman sanya sauran kasashe kulawa da hakkin dan Adam, maimakon su da kansu su yi haka.

Batun nan ya shaida gaskiyar wata tsohuwar magana dake cewa: “A yi bincike kan halayyar wani mutum bisa aikace-aikacensa, maimakon kalmomin da ya fada”. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Ya Kamata Kasashen Yamma Su Yi Hangen Nesa Game Da Tasirin Rikicin Ukraine Kan Kasashe Masu Tasowa

Ya Kamata Kasashen Yamma Su Yi Hangen Nesa Game Da Tasirin Rikicin Ukraine Kan Kasashe Masu Tasowa

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version