A wata sabuwa, ƙungiyar fafutukar ‘yan ta-ware na biyafara ta ƙaryata tsegumin tsohon gwamnan Jihar Abiya, Dakta Orji Uzor Kalu, cewar shugabanta Mazi Nnamdi Kanu ya tsere zuwa ƙasar Ingila, inda kuma a yayin tserewar ya bi ta ƙasar Malesiya. Ƙungiyar ta jaddada cewar tun lokacin da sojoji suka kawo samame gidan Kanu, har suka kashe wasu daga cikin iyalanshi, babu wanda ya ƙara jin ɗuriyar sa.
Daga Idris Aliyu Daudawa, Abuja
Ƙungiyar IPOB ta ce lauyoyinta za su matsa Dakta Kalu a gaban alƙali domin ya bayyana gaban kotu don maimaita wannan batu da ya kawo, wato duk wasu abubuwa da ya sani dangane da inda shugaban IPOB ɗin yake; sun ce Kalu zai yi wannan bayanin ne a yayin da aka fara sauraren ƙarar da suka shigar a babbar kotu ta Abuja.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar, Emma Powerful, wanda kuma ya ƙara da cewa, yanzu dai ana ta yaɗa jita-jita ne, musamman ma zantukan da Dakta Orji Uzor Kalu.
“Mu dama tuni mun yi shirin sauraron maganganun da basu dace ba, waɗanda za a riƙa yi ma ‘yan kabilar Ibo, manufa a nan, yadda ake ta yin maganganu na ɓatanci akan su, ga kuma sayar da ‘yancinsu wanda tuni aka yi. Bugu da ƙari ga kuma maganar fafutukar kafa Biyafara, ko shakka babu ai yanzu mu mun san ko su wanene Karnukan farautarsu waɗanda su ba damuwarsu bace, idan dai har za a cika masu aljihunsu, za su iya yin komai.” Inji shi
Emma Powerful ya ci gaba da cewa: “Irinsu Orji Kalu ba wani abin da ya dame su musamman ma, yadda suka haɗa baki da Sojoji har abin yayi sanadiyyar mutuwa da kuma raunata wa da nakasa wasu ‘yan uwanmu. Ba damuwarsu bace, idan dai har cika masu muradansu. Su mutane ne da basu ɗauki ‘yan uwansu da muhimmanci ba, su ne za su iya sayar da mutuncin su, ba kuma damuwarsu ce ba don za a wulaƙanta ‘yan uwansu. Mu dai a iya sanin mu tun bayan mamayan da sojoji suka yi mana a harin 11 ga watan Satumba ba mu ƙara jin ɗuriyar shugabanmu Kanu ba.
“Ƙasashen Ingila da Malesiya ai ƙasashe ne waɗanda sun daɗe da wayewa da kuma goguwa, bayan haka kuma su ba maganar karɓar rashawa da cin hanci kamar Nijeriya, domin kuwa ba a da ƙiyasin ko mutane nawa ne suka bar ƙasar da kuma shigo cikinta. Abin da shi Uzor Kalu y ace kamar ya ƙaryata shugabannin ƙasashen ne, lokaci da suka nemi da a basu labarin wurin da Nnamdi Kanu yake , kuma wane hali yake ciki.
“Ga waɗanda basu san yadda ƙasar Ingila take ba, ita fa wani wuri ne wanda yake tsibiri wanda ruwa ya zagaye. Da kuma matuƙar wuya mutum ya shiga irin wannan wuri ba tare da an gane shi ba, mun dai lura yanzu ana ta ƙoƙarin waneene zai kasance jagaba a jerin waɗanda ke sayar da mutuncin al’ummarsu, wato daga cikin masu kiran kansu shugabannin ƙabilar Ibo, sun kasance ‘yan lelan Hausa Fulani ne.’’ inji sakataren
Daga ƙarshe Ƙungiyar IPOB ta ce za ta bi ta hannun lauyoyinta domin Orji Kalu da Buratai su bayyana a kotu ranar 17 ga watan Oktoba 2017, su faɗawa duniya wurin da Nnamdi Kanu ya ke. “Abin dariya ne wai a ce shugabanmu yana Ingila, wannan ya nuna kenan tun farko ashe dama haɗin baki ne aka yi da gwamnoni irinsu Okeozie Ikpeazu, Willie Obiano, Rochas Okorocha, da dai sauran wasu manyan ‘yan siyasa na ƙkabilar Ibo, domin kawai a halaka ‘yan ƙabilar don a faranta ma ‘yan arewa zuciya. Ko ba haka bane?”
“Duk wani mai hankali abin zai ba shi mamaki ta yadda shi Uzor Kalu yake ta kai gwauro ya kai mari domin dai kawai ya samu cimma burinsa, bayan kuma shi ɗin yana da wata babbar matsala ta gida, wadda ta shafi asalin shi. Sai ga shi kuma yanzu shi ne ke neman ya farantawa gwamnatin Nijeriya rai.
“Tambayar da muke son shi Uzor Kalu ya bada amsa ita ce, idan shi ɗan Nnanna Kalu ne, mi yasa ya faɗawa mutane cewa shi daga Igbere yake, amma kuma mutumin da yake cewar shi mahaifinsa ne, ba daga can yake ba. Shugabanmu Mazi Nnamdi Kanu kafin Sojoji su yi awan gaba da shi , ya kawo ƙarshen yin siyasa ta jari hujja, wadda ake bada kai Bori ya hau musamman ga shugabannin siyasar Arewa, abin kuma an san daga ƙarshe zai kawo ma ’yan ƙabilar Ibo koma baya. Shi yasa ai yaƙi ya amshi abin goro daga Kalu, saboda an tsaya kamar tsayuwar wata sai an samu’yancin ‘yan biyafara. Mun kuma gode da ka nuna shugabanmu ba a iya sayen shi da kuɗi saboda daga ƙarshe abin ba zai faɗi ba. Maganar siyasa ta sayar da ‘yancin Kudu maso gabas ga shugabannin siyasar Arewa waɗanda ke riƙe da muƙaman gwamnati, shi ya sa aka samu haɗin kai na ƙoƙarin ganin ko ta wane hali an kashe Nnamdi Kanu, a kuma soke ƙungiyar biyafara, wanda aka yi sa’a, yanzu ƙoƙari ake domin a ce ba hannun soja a kisan gillar da aka yi wa ‘yan kabilar Ibo.” In ji Ƙungiyar