Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja
Kungiyar Kwadago ta ULC, wacce ta ke kishiyantar kungiyar NLC, za ta fada yajin aiki daga yau Litinin 18 ga Satumbar 2017, matukar ba an shawo kan wata yarjejeniya da aka cimma akan bukatun da tace ta gabatarwa gwamnati tun cikin watannin baya ba.
Cikin kungiyoyin da suke a karkashin wannan kungiyar ta ULC har da NUPENG, masu dakon man fetur, da ma’aikatan wutar lantarki da bankuna da kuma matuka jiragen sama da na kasa da dai sauranasu.
Duk da gargadin da gwamnatin tarayya ta yiwa kungiyar kwadago ta ULC ‘United Labour Congress’, kungiyar ta ce babu wani barazana da zai yi musu tasiri har su janye yajin aikin da zasu fara a yau Litinin.
Ya ce, “Wannan yajin aiki, duk da ba kaunarsa muke ba, shi ne kadai matakin da zamu iya dauka. Mun yi iyaka kokarinmu wurin bin hanyoyin sulhu don magance matsalar, amma hakan bai yiwu ba.
“A dalilin haka muke kiran ‘yan kasa masu kishin kasa da su bamu hadin kai domin tunasar da gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi akan su yi adalci wurin sauke nauyin da ke rataye a wuyansu.”
Shi ma Sakataren tsare-tsare na kungiyar kwadago ta ULC, Kwamared Nasir Kabir, ya bayyanawa manema labarai cewa kadan daga matsalolinsu har da Ministan Kwadago, Dakta Ngige, wanda ya ce yana nuna son zuciya, ta wajen fifita kungiyar NLC, domin ya ki ya saki lasisin rijistar kungiyar ta ULC, da kuma rashin biyan ma’aikata albashinsu da gwamnonin jihohi suke yi.
A daya bangaren kuwa, yayin da yake sharhi kan illar yajin aiki ire-iren wannan ga tattalin arzikin kasa, shugaban sashen koyon ilmin tattalin arziki da dabarun kasuwanci a kwalejin kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, Dakta Lawal Habeeb Yahya, ya ce hakan zai sake mayar da hannun agogo baya, ga tattalin arzikin da yake kokarin tsamo kan shi daga koma bayan da ya shiga, shekaru biyu da suka wuce.
Sai dai ya zuwa hada wannan rahoton, duk wani kokari da wakilinmu yayi don jin matsayar ma’aikatar Kwadagon Nijeriya, abin ya ci tura.