Batun Yawaitar Haduran Ababen Hawa A Nijeriya (I)

Ababen Hawa

PIC.15. SCENE OF AN ACCIDENT AT BRT BUS STOP, FADEYI, ON IKORODU ROAD IN LAGOS ON FRIDAY (3/6/16). 4009/03/6/2016/WAS/CH/NAN

Saboda yau da gobe, sai ya zamana cewa, ba mutane ne kadai ba cikin wannan Kasa ta Najeriya ba, su ka san hadari bisa titunan Kasar ba, a’a, hatta ma wasu rukuni daga cikin dabbobi, san hadari, sun fahimce shi, kuma ma suna gudunsa dare da rana, misali, AKUYA. Babu sabani, dabba Akuya, ta fi dabba Tinkiya sanin hakikar hadari a kan titi, kuma ta fi ta yunkurin kauce masa a aikace.

Tun da hatta ma har cikin dabbobinmu na gida, akwai wadanda suka fahimci abinda ake nufi da hadari tare da yunkurin kauce masa, ke nan zai zama tamkar asarar kalmomi, idan a ka tasamma yi wa mai karatu ta’arifin kalmar hadari. Ma’ana, a ka yi kokarin fassara masa hakikanin ma’anar kalmar ta HADARI. Sai dai duk da haka, kara tunasar da mutane wani abu da suka sani tuntuni, hakan ba zai zamto wani aikata laifi ba. A takaice;

“…Yayinda aka sami wata taho-mu-gama a tsakanin mai mota da mai mota, ko mai mota da mai babur, ko mai babur da mai babur, ko mai keke da mai babur, ko mai keke da mai mota, koko mai keke da mai keke, ko kuwa, a tsakanin mutumin dake tafe bisa hanya, ko yake zaune a gefen hanya, ko ya zo tsallaka hanya, amma ya rafka karo (ko suka bangaje shi) da wani mai mota, ko mai babur da sauransu, wannan kaftar juna a tsakanin ababe biyu a bisa hanya, shi ne ake nufi da kalmar hadari…”.

A duk cikin sasanni da nahiyoyin Duniya, babu inda babu inda ba a yin hadari. Sai dai, akwai hadari na ganganci, na sake da tsabar son zuciya, wadanda suka zama ruwan-dare a cikin wasu lardinan Duniya. Cikin wasu lardinan kuwa, irin wadancan haduran da za a iya kauce musu, ba su faye afkuwa a cikinsu ba, sai dan abinda ba za a rasa ba na ajizancin Dan’adam. Babban abu ma fi muni shi ne, a wasu Kasashen Duniya a yau, musamman cikin nahiyar Afurka, yunkurin hakkewa afkuwar haduran, tamkar wani salo ne abin-birgewa wanda ba kowane ya gwanance masa ba.

Cigaba Da Afkuwar Hadura A Sasannin Duniya

Batun afkuwar haduran ababen hawa, tuni ne ya zamto babbar annoba ga Kasashen Duniya, musamman a yankin kasashen Afurka na kudancin Sahara.

Binciken masana ya hakkake cewa, a duk Shekara cikin Kasashen Duniya, a kan sami adadin mutane miliyan guda ne da dubu dari uku da talatin da biyar (1.35m) wadanda ke kwanta dama a sanadiyyar miyagun hadarirrika da ake haduwa da su bisa hanyoyi a tsakanin ababen hawa.

 

Masanan, sun sake tabbatar da cewa, miyagun raunukan da a yau Duniya ke fuskanta a sanadiyyar hadura bisa tituna, su ne kan-gaba wajen hallaka kananan yara “yan Shekaru zuwa biyar(5), da kuma samari matasa wadanda Shekarunsu na haihuwa ba su gaza ashirin da tara (29)ba. Kashi ashirin da shida bisa dari (26%) na wadanda hadarirrikan ke hallakarwa, su ne mutanen da ke tafe bisa hanya a kas, da kuma wadanda ke tafe bisa kekuna. Kashi ashirin da takwas bisa dari (28%) na masu rasa rayukansu a sanadiyyar hadarirrikan, masu tuka babura ne da kuma fasinjoji.

Kasashen Da Ke Da Raunin Tattalin Arzikin Kasa Ne Haduran Su Ka Fi Kassarawa A Duniya

Dalilai masu tarin yawa da sai nan gaba ne cikin wannan rubutu za a zayyano su, su za su hakkake hujjojin da suka sanya al’umar Kasashe masu tasowa, cikinsu har da tarayyar Najeriya, haduran su ka fi kassarawa sama da al’umar nahiyar Turai da makamantansu.

Bayanan masu bincike ya tabbatar da cewa, miyagun hadarirrikan dake kaiwa zuwa ga salwantar rayuka da a ke fuskanta a Kasashe masu raunin tattalin arzikin Kasa, ya ninka uku ne, a kan irin wadanda ake samu a Kasashen dake da bunkasar tattalin arzikin Kasa a Duniya. Sai dai an fi samun yawaitar haduran ne a Kasashen Afurka. Duk cikin mutane dubu dari (100,000) dake shekawa barzahu a dalilin haduran, kashi ashirin da shida da digo shida (26.6) “yan Kasashen Afurka ne. Sannan, cikin wancan adadin (100,000) na wadanda ke rasuwar, kashi tara da digo uku (9.3) ne suka fito daga yankin nahiyar Turai bakidaya.

Daga Haduran Ababen Hawa A Najeriya

Kididdigar masana na cewa, a duk Shekara a Najeriya, akalla mutane dubu talatin da tara (39,000) ne ke bakuntar-lahira a sanadiyyar haduran kan tituna. Bugu da kari, a cikin Shekarar 2018, wani rahoto karkashin hukumar lafiya ta Duniya (WHO), ya tabbatar da cewa, cikin waccan Shekara ta 2018, mutane dubu talatin da tara da dari takwas da biyu (39,802) ne suka mutu, sakamakon haduran kan titinan Najeriya. Sai hakan ke nuna cewa, duk cikin mutane dubu dari (100,000) da ke mutuwa a fadin Duniya sakamakon haduran ababen hawa, kashi ashirin da daya da digo hudu (21.4) “yan Najeriya ne.

Exit mobile version