Bauchi, " />

Bauchi Ta Ware Miliyan N10 Don Feshin Korona A Jihar

Gwamnatin jihar Bauchi ta ware zunzurutun Naira miliyan 10 domin yin feshin sinadarin dakile yaduwar cutar Koronabairus a jihar.

Kwamishinan muhalli da gidaje na jihar, Honourable Hamisu Muazu Shira, shine ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da manema labaru lokacin kaddamar da fara aikin feshin da suka yi a cikin makon da ya gabata.

Kwamishinan ya shaida cewar feshin na tsawon kwanaki biyar an tsara yi ne a layuka da sassan da suke fadin cikin birnin Bauchi domin yaki da cutar numfashi mai hanzarin yaduwa.

“Mun kasance a nan ne domin kaddamar da yin feshi kan cutar Koronabairus a jihar, inda gwamnatin jihar ta karfafemu wurin gudanarwa.

“Gwamna Bala Muhammad ya tabbatar da aniyarsa na taimakawa aikin domin tabbatar da kare jama’an jihar daga annobar da ke bazuwa a sassan duniya,”

Hamisu Muazu Shira sai kuma ya shaida cewar za a iya fadada aikin feshin zuwa wasu sassan jihar dukka dai a cikin kokarin yaki da cutar.

Ya ce, sama da mutum 300 ne suke kan gudanar da wannan aikin, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki da su bada tasu gudunmawar domin cimma nasarar aikin.

Exit mobile version