Shi da ma wani lokaci haka shi al’amari yake kasancewa musamman ma wanda aka ce ya shafi lafiyar al’umma ne hakanan ma idan aka yi la’akari da yadda ita annobar cutar ta Korona ta kasance a duniya, wadda ta fara bulla ne a su kasashen Turai a karshen shekarar 2019, sauran wasu nahiyoyin kamar Afirka tsakanin karshen watannin Janairu da kuma farkon watan Fabrairu ne na wannan shekara ta 2020, ta gallabi da kuma ta’azzari kasashe masu yawa, ba ma kamar irin kasashen da suka ci gaba ta hanyoyi daban daban na rayuwa. An yi asarar rayukan mutane masu yawa wanda kuma kasashen da abin ya fi shafa su ne na ’yammacin Turai, inda bayan ma ga ita rasuwar ta al’umma da akwai maganar karewar tattalin arziki.
Ba za a ce ita nahiyar Afirka abin bai shafe- ta ba ko shakka babu abin ya shafe ta matuka musamman ma ta bangaren tattalin arzikin kasashen wanda dama can yana tangal tangal ne duk dai a sanadiyar ita wannan cutar ta Korona. Koda- yake dama su masana sun yi hasashen cewar tana iya yin kamar shekara biyu kafin ace tayi sallama ta bar kowa ya samu ya mike kafarsa.
Har ya zuwa wannan lokacin da muke ciki da ita annobar ta sake bullowa ko kuma kunno kai, da akwai kasashen da basu kare murmurewa ba daga cutar. Sai dai kuma wani al’amari da yake ba daban ne shi ne wanda ya shafi maganin da aka samu na rigakafin ita cutar ta Korona, ya kasance wani abin farin cikin ko kuma murna zan iya cewa idan aka yi la’akari da yadda ita cutar ta yi sanadiyar rasuwar mutane da kuma faduwar tattalin arzikin duniya.
Amma kuma wannan kamar ana iya cewar ‘Yaro bari murna domin Karen ka ya kama zaki to zaki mana idan aka yi la’akari da wasu nakasu-nakasun da suke tattare da shi maganin wadanda kuma daga can kasar ta Ingila ce abin ya fito. Kafin dai bayyanar shi wannan al’amari mai daure kai, dama da akwai wadansu kasashe wadanda bama na nahiyar Afirka ba kadai sun fara yin dari-dari da shi maganin rigakafin allurar cutar Korona.
Wannan shi ne abinnan da masu iya magana ke cewa, “Huta roro da waken gizo ya ki yin ‘ya’ya” abin boye dai ya fito fili ke nan tunda dai nau’in cutar Korona na wannan lokacin na kasar Birtaniya shi ne wanda yafi muni sai kuma ga shi bayanan nakasun maganin daga can ne suka fito sai yaya ke nan.
Saurin ma me ake yi ne wajen bincike da kuma amince ta ita wannan allurar rigakafin domin kuwa ita irin wannan allurar ta rigakafi, zuwa shekarar 1960 akan dauki shekaru hudu ne ana yin aiki kafin a samar da wata allurar rigakafi. Ita kuwa wannan allurar rigakafin cutar Korona kasa da shekara daya ne aka kikiro ta, amma har aka samu amincewa ayi amfani da ita ga al’ummar duniya. Shi duk wani al’amari wanda na gaggawa ne baya haifar da mai ido, sai dai daga baya a rika yin dana-sani.
Ana iya tunawa fa da yadda aka kare da rikita- rikitar allurar rigakafin cutar Shan- Inna ko kuma Poliyo da gwamnatin jihar Kano wanda abin sai daya kai ga shigar da karar shi kamfanin na Pfizer ranar 3 ga watan Afrilu 2003, lokacin da yara daga iyalai talatin suka kamu da wasu illolin cutar dat shafi jikinsu.
Gwamnatin ta nemi da a biyata kudi Dalar Amurka bilyan bakwai saboda allurar da aka yi amfani da ita wajen yi ma yara rigakafin bata da kyau ta hakan ne kuma suka kamu da nakasa daban daban, wancan lokacin ma ke nan da shi kamfanin bai ce ba zai ki biyan duk wani abinda aka ce ba koda kuwa an hadu da wata matsala. Wannan lokaci dai karara su Kamfanonin biyu suka ce ba wani abinda za su iya yi koda an hadu da wata matsala.
Akwai wani al’amari wanda shi ma yana da kyau ayi nazarin sa inda aka ce koda an yi wa mutane ita allurar ta rigakafin wannan ba zai hana su kamuwa da cutar ba, ai shi ake kira da suna wani hanzari ba gudu ba, ai tun farko bai ma dace ba ace an yi ma wsu allurar ba muddin ba za ta hana su kamuwa da cutar ba.
Akwai dai wani shahararren kamfani wanda na hada magunguna ne mafi shahara a duniya da kuma fice wanda ake kira da suna Pfizer yana kuma da kamfanin sa wanda yake yin harkokin sa a kasar Amurka, shi ne ya samar da allurar rigakafin ta annobar cutar Korona, amma kamfanin bai iya daukar wani alkawari ba wani alhakin duk abinda ya biyo baya ba, ko faru wanda na illa ce ga mutane ba, bayan an yi masu amfani da shi a rigakafin na Korona.
Wata ayar tambaya anan ita ce shin ko Hukumar lafiya ta duniya ta san da su illolin maganin aka kuma amince duniya gaba daya tayi amfani dasu, wannan kuma ganin cewar ga fa illolin wadanda kuma an bayyana su karara, duk kuma wanda ke so zai iya shiga ta yanar gizo ya karanta. Za su kasance illa ga al’umma daga karshe amma kuma sai ga shi an amince ayi amfani dasu, duk kuwa da yake za su iya mummunar illah, domin kuwa idan aka kalli shi al’amarin ta wani nau’in fasahar sai wani tunani ya zo ko ana bukatar a rage yawan al’umma ne na wani sashe.
Abin ba anan kadai ya tsaya ba domin kuwa akwai wani babban kamfanin hada magunguna da ake kira Bio pharmaceutical New Technologies (BioNTech) dai shi kamfanin mallakin kasar Jamus ne shi-ma ya samar da rigakafin cutar, haka nan shi ma bai yi alkawarin daukar alhakin illolin da rigakafin da maganin allurar zai iya haifarwa ba ga mutanen da aka yi wa ita allurar rigakafin.
Ga ma wasu bayanai 11 da aka wallafa a wani shafin yanar gizo na ita gwamnatin kasar Ingila, dangane da ita allurar wanda kuma duk yake da bukatar ko sha’awar karanta su bayanan da turanci yana iya shiga nan, saboda kuwa ai Hausawa sun ce gani ya kori ji, haka nan ma gani da ido ai maganin tambaya ne.
(1) Allurar Rigakafin Korona da aka samar zata haifar da illa ga mata masu juna biyu.
(2) Allurar zata iya haifar da illa wajen hana mata daukar ciki na tsawon watanni bayan an yi masu ita allurar.
(3) Allurar za ta haifar da illa ga mutanen da suke da matsala ta rashin karfin garkuwar jiki.
(4) Babu wani bincike ko gwaji akan tsawon lokaci da allurar rigakafin zata iya dauka a jikin mutum da kuma irin illolin da zata iya haifarwa.
(5) Babu wani gwaji da akayi don a samu gano girman illar da rigakafin zai iya haifarwa, kamar sauran allurai da suke haifar da illa wadanda domin haka ne aka haramta su.
(6) Babu wani tabbacin cewar ko ita allurar ba zata iya kashe kwayoyin halittar haihuwa da suke jikin mutane ba.
(7) Idan an yi wa mutane allurar rigakafin ba zata iya hana su kamuwa da cutar Korona ba.
(8) Idan an yi wa mutumin da yake dauke da cutar Korona allurar rigakafin ba zata hana shi ya yada cutar ba.
(9) Mata masu shayarwa idan an yi masu allurar ba za su ci gaba da shayarwa ba saboda hadarinta ga jarirai.
(10) Ba a yi gwajin allurar rigakafin kan kananan yara ba, kuma allurar ba zata dace da yaran da suke kasa da shekaru goma sha shida ba.
(11) Gwamnatin Ingila da kamfanin da suka samar da allurar rigakafin Korona babu daga cikin su wanda ya yi alkawarin daukar nauyi akan biyan wata diyya ga duk wanda aka yi wa allurar rigakafin ta yi masa illa.
Dalilin Da Ke Kawo Zubewar Gashin Mata
Shekaru masu yawa da aka fara yin gyaran gashi, da...