Connect with us

LABARAI

Baya Ta Haihu: Masu Garkuwa Sun Dawo Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

Published

on

Sun Kashe Matafiya Tare Da Sace Da Dama
A ranar asabar ne ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane suka bude wa matafiya wuta a kusa da garin Jere a kan babban hanyar Abuja zuwa Kaduna, kamar yadda majiyarmu DAILY NIGERIAN ta bayanna, ta ce, masu garkuwa da mutanen sun kashe mutum biyu yayin da kuma suka yi awon gaba da jama’a da dama a matsayin garkuwa.
A ranar 22 ga watan Yuli ne, masu garkuwa da mutane suka kashe wata Farfesa da wasu jami’an soja da ‘yan sanda bayan da suka yi garkuwa da wasu da dama a kauyen Gidan Busa, dake a tsakanin garin Jere da Kateri a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Wanda harin na baya bayan na ya rutsa da shi, mai suna Abubakar Barau, ya bayyana wa kafar watsa labarai ta DAILY NIGERIAN cewa, masu garkuwar sun fado kan hanya ne inda suka shiga harbin kan mai uwa da wabi a kan motoci dake wucewa.
“Na taso ne daga garin Zaria zuwa Abuja a dai dai karfe 5 na yamma, bayan na wuce wata mota bas, na ga wasu mutum 3 a kan titi, muna kusa dasu kawai suka bude mana wuta ba tare da sun bukaci mu tsaya ba.
“Nan take na yi ta kan daya daga cikinsu, inda suka ci gaba bude wuta, a nan ne na lura inda mun tsaya za su kashe mune kawai sai na yi ta gudu, mun yi nasarar tsira amma dai motarmu ta sha albarushi.
“Da muka isa garin Kateri ne muka yi wa ‘yan sanda rahoton abin daya faru muka kuma canza tayan da suka fasa mana.
“Abin takaicin shi ne, ‘yan sanda suka ce basu iya fuskantarsu, suka shawarce mu mu gaggauta canza tayanmu mu bar wajen.
“A yayin da muke canza tayan, mun lura da cewa, babu wasu motocin dake zirga zirga abin dake nuna alamun lallai sun tare motoci masu wucewa kunan.
“Daga baya muka samu labarin sun kashe mutum 2 sun kuma yi garkuwa da wasu da dama,” inji majiyar jaridar DAILY NIGERIAN.
Jami’in watsa labaran rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya tabbatar da rasuwar matafiya 2 a harin da ‘yan ta;addan suka kai, ya kara da cewa, nan take ‘yan sanda suka aika da rundunarsu wajen da abin ya auku.
“Sun bude wuta akan matafiya da misalin karfe 6 na yamma, nan da nan mutanen mu suka hai dauki wajen da aka kai harin in da aka samu ceto wani direban mota Bus da suke kokarin yin garkuwa da shi.” Inji shi.
Advertisement

labarai