Connect with us

LABARAI

Bayan Ƙaryata Samuwar Cutar Korona, Shugaban Brazil Ya Kamu

Published

on

Sakamakon gwajin da aka yiwa Shugaban Kasar Brazil, wanda aka yi masa a ranar Litinin bayan nuna alamun kamuwa da cutar Korona, ya tabbatar da cewa shugaban na dauke da cutar.

Bolsonaro ya sha nuna wannan cutar ba wata aba ba ce, yana kiranta ‘yar karamar mura yana kuma cewa baza ta taɓa kwantar da shi ba.

Ya kuma umarci gwamnonin yanki da su sassauta dokar kullen da aka sanya saboda shawo kan annobar Korona, wanda ya ce tana hana ci gaban tattalin arziki, a jiya Litinin ne kuma ya sassauta dokar sanya takunkumi.
Advertisement

labarai