Hassan Hamza" />

Bayan Azumi Mu Tashi Tsaye (2)

Ci gaba daga makon jiya

6. Muyi hattara da abokanta: dole ne mutum ya yi abokai. Hakan yana cikin ma tsarin gudanar da rayuwa. To amma zamani ya kawomu wani haddi da yawancin abota takan kaimu ta baro.

Abokai da yawa ayau sukan kai ga halaka. Yawanci bakayi niyyan yin wani abu ba amma abokai zasu sa ka. Kaga hakan kuwa ba kyau musamman ma idan yin hakan zai kai kai ga sabawa Allah. Dole ne ko wannenmu ya zama yana da iyaka a yin komai a rayuwa. Kuma duk inda kake son ka tsaya ba nan abokinka zai so yatsaya ba. Sai ka dawo kabarsu su tafi. Wani lokaci ma za ta kama ka canza abokai kamar yadda kake canza riga. Ya yi, idan kayi hakan ne domin kiyaye iyakan da Allah ya shinfida maka.

7. Mu rike iyaye: idan iyayenka suna da rai ka ji dadi. Amma kuma kayi kokarin moran rayuwarsu tun kafin karasa su. Ka taimaka musu, ka lura da cinsu da shansu. Kabiya duk bukatunsu tun basu taso ba. Kayi musu ladabi da biyayya matuka. Ka bisu a hankali. Kabi umurninsu. Kayi musu addu’a kuma ka nemi taimakon Allah a rayuwarsu.

Idan ka rasa iya yenka to sannu, sai ka rika yi musu addu’a a kullum. Ka kuma yin sadaka da sunansu. Sannan ka rike kayi alheri wa iyayen wassu. Idan kayi hakan kaman kayi wa iyayenka ne.

8. Mu Ciyar da Iyali:  wallahi yawancin masifu dake samunmu yana tattare ne da irin wulakanta iyalinmu da mukeyi, muna barinsu da yunwa. Allah yakan bamu amma muna yawanta fadin babu kullum a gida. Babu kyau hakan. Gida shi ne a farko. Duk inda gida yana cikin halin bukata babu kai ba zama ba kwanciyar hankali.

Koman kankancin abun hannunmu mu bayar wa iyali. Amma duk inda mukace babu alhali kuwa akwai to musani sai karin talauci muke dora wa kanmu. A cikin bayar wa iyali ne arzikinmu ke karuwa.

9. Mu bar yi da mutum: hakkin dan adam nauyi ne dashi. Mu guji daukan hakkin mutane. Tsakaninka da mutum salun alun. Idan baka bashi ba kada ka dau kayanshi ko hakkinshi. Allah baya yafe hakkin wani sai idan mai shi ya ya yafe. Allah kuma baya son a taba hakkin bayinsa komai addini ko kabila ko jinsi ko asali ko launinsu.

Yaudara da gulma da cin zarafi da zagon kasa, da annamimanci da zagi da ta’addanci da sata da zamba cikin amincin ababe ne da suke hada mu da mutane da shiga cikin hakkin mutane. Kuma duk inda aka samemu acikinsu muna nan jingim da hakkin mutane da mukewa. Irin hakan ne yake tarwatsa rayuwarmu ya rage arzikinmu ya jawo mana masifan cuta da na tashin hankali arayuwarmu amma ba tare da munsan hakan ba. A gun Alla duk yan adam abu daya ne. Gara ka dauka haka ka tafi dasu lafiya da sannu.

10. Mu fita hakkin shugabanni: shugabanci ba karya bane ba. Shugabanci babban al’amari ne agun Allah kuma Allah yana son mai girmama shugaba. Shiyasa ma tuni ya ce, mubi shi mubi annabi sa’annan mubi shugabanni.

Da shugaba da mabiya duka suna da hakkin juna akansu. Kuma acikin halin dangantaka ta gudanar da harkar mulki, hukunci mai tsanani ne yake shiga tsakani.

Yawancinmu a Nijeriya mukan dauka shugabanni ne kawai azzalumai a ko yaushe. Ba haka bane. Babban zalunci ma yanzu a mabiya yake. Shiyasa shugabanni basa mana adalci da muke nema.

Dole ne sai mun girmama Allah da manzonsa da shugabanninmu sannan Allah zai yi mana rahama da shugabanci. Idan sun ce muyi muyi. Idan sunce mu bari mubari.

Sai gashi Baba Buhari yana cewa my gyara, mu bari, mu canza, amma nawa acikinmu munbi umurninshi? Wannan ma Baba Buhari ne fa? Ina ga wani shugaban da kana ganinsa azzalumi ne? Mu daina zargin kowa da zalunci alhal muna nan tsundum a cikin zalunci.

Ba ruwanka da zaluncin da wani yake yi. Allah ne maganin azzalumi. Barshi da shi. Yafi dadi.

Amma kai ka tabbata ba kayi zaluncin ba. Allah yasa ana zaluntanka a maimakon kai kayi zalunci.

11. Muguji daukan/lalata kayan hukuma: kayan hukuma kayan al’umma ne, kayan duka ne, kayan kowa da kowa,  kayanmu ne duka, kuma kayan amana, kayan Allah ne. A duk inda muka sami kayan hukuma a hannunmu, wajen aiki ko a gefen hanya, yana kaman amana ne agunmu. Mu rike su da hankali kaman namu, muyi anfani dasu, muyi aikin gwamnati ne kawai banda aikin kanmu.

Mu lura da lafiyarsu, mukula da tsawon ransu kada muyi saurin lalatasu kawai domin ai gwamnati za ta sayo wani. Idan naka ne ya za kaji da saya? Hakan kuma almubazzaranci ne da ka keyi da dukiyar jama’a. Mu rika yin tanadi da kayan gwamnati. Idan da tanadi gwamnati za ta iya yin abu dayawa da kudi kadan.

12. Mu tashi da himma a kan hukatun wassu ma: duk mai jin nauyin mutane kuma zai tashi da himma akan bukatunsu yana tare da rahamar Allah da manzonsa. Kuma a duk tasowan bukatarka Allah ne mai kawo maka agaji. To amma kuma dole ne mu nemi taimakon mutane.

Idan muna neman rahama da taimakon Allah a rayuwarmu dole ne mudau himma a kan sauraron bukatun yan uwa musamman idan sun zo mana dasu, kuma muyi yunkurin taimakawa koda ba duka, ba ko ba a kullum ba.

Muhimmin abu dai zuciya tayi niyyan hakan. Allah zai gani niyyar taimako da kayi koda baka da ikon yi. Mu nuna damuwa da tashin hankali akan matsalolin wassu ba sai kawai namu matsalar ba. Idan munyi haka Allah ne da kansa zai tashi da himma a kan namu bukatun. Dukkan rai abu guda ne. Yadda kake ji idan kana cikin kunci ko walwala haka kowa yana ji. Saboda haka muji wa yanuwa halinsu kuma mu nuna halin taimako iyaka kokarinmu na dan adam.

Allah yasa sabbin gwamnoni da jagororinmu da muka zaba su zama mana masu tausayin al’umma da so mata gyara da ci gaba wajen samowa ababen mora rayuwa. Allah yasa mu ma zamu tashi mutaimaka musu a kan hakan da zuciya daya domin Allah.

Exit mobile version