Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home Uncategorized

Bayan Bude Kan Iyakoki Da Sauran Aiki, In Ji Gambo Danpass 

by Muhammad
December 30, 2020
in Uncategorized
3 min read
Iyakoki
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daya daga cikin ‘yan kasuwar Jihar Kano kuma  Basarake, a gefe kuma dan siyasa mai sharhi a kafofin yada labarai na gida da waje Alhaji Muhammadu Abdullahi  Gambo Dan pass Dan Saran Kano, ba bako bane wajen bayyana ra’ayinsa da ba da shawara ga gwamnati  domin a samu gyara. Wannan karon ma Allah ya sake hada shi da Wakilin LEADERSHIP A YAU, HARUNA AKARADA, inda suka tattauna dangane da wasu abubuwa da suka taso kuma game da abin da yake faruwa a yankin Arewa, ga yadda hirar ta kasance.

 

samndaads

Kusan abubuwa da ke zagayawa a wannan makon shi ne batun na bude kan iyakoki guda hudu da gwamnatin shugaba Buhari ta yi, kuma wannan abu ne da kowa yake fadar albarkacin bakinsa ganin cewa wasu sun zuba jarinsu a shinkafar gida kuma bude kan iyakoki ka iya jawo musu babbar asara, ya ya kake kallon wannan al’amari?

To, gaskiya babu abin da za mu ce da Allah sai godiya, dama mun dade muna kiraye-kirayen cewa a bude kan iyaka. Na san tun da akwai gwamnati ga jami’an tsaro duk abin da ba’a so a kawo na san za a dau mataki a kan haka, kuma duk abin da ya dame mu shi ne rashin hadin kan ‘yan Arewa daidai da wannan kogi da aka ce za’a kawo ya kasa gamuwa wannan abin takaici ne. Kuma mu ‘yan Arewa mun zama tsintsiyar shara, kai sharar ma ba ma yi duka yanzu manyan Arewa a ce shugaban kasa ya kasa jin kukansu babu takaicin da ya fi wannan. Muna kira ga shugaban kasa da ya kira taro na ‘yan Arewa a tattauna abin da zai yiwu kada Dimukradiyya ta cinye mu ga harkar tsaron nan ta addabi Arewa gaskiya babu kasar da za ta zauna da talauci a zauna lafiya.

 

Irin wannan matsalolin da suke faruwa a nan Arewa, bas a faruwa a Kudancin Kasar nan, domin idan za ka je can za ka suna magana da murya daya ce me ya sa haka?

To, ai ba ma ‘yan Kudu ba, a nan din ma an raba mu kowa ya ja nasa babu abin da ake yi sai karya an wargaza Arewa babu mai son dan uwansa sai gaba kawai muna kashe kanmu ko wannan titin Kano zuwa Abuja Ministan ayyuka ya ce wai za’a gama nan da wata takwas ba a gama ba, me ya kawo wannan matsalar, amma na Lagos da Ondo da Osun ai tuni an gama. Ya kamata gwamnati ta sa a bincika sosai a kan wannan lamarin hanya guda daya kawai, kirana ga shugaban kasa ya sani Wallahi bamu da komai a Arewa.

 

Akwai tsarin shigo da kaya Arewa, ko hanyar da aka tsara ne ya sa komai baya sauki ko da an kawo shi daga waje?

Ai rashin wadatar abu ne yake kawo tsadar kaya shi ya sa wannan rufe kan iyakar ba karamin cutar wa ya yi ba, ga lalacewar masana’antunmu.Yanzu in ka duba Sharada ko Dakata ina masana’antunmu babu, sai kadan ne kawai suke aiki ko Chalawa ina masana’antun babu, duk dan Arewa idan ya sami mukami sai ya kasa komai amma idan wani ba dan Arewa ba sai kaga komai yana tafiya daidai me ya same mu ‘yan Arewa.

 

Rashin hadin kan duk al’unmar da bata da hadin kai sunanta wargajajjiya, ya kamata a gayawa gwamnoni su dinga kula ba su dinga tumur-musa talakawan su ba wannan bai dace ba. Duk kasar nan, nan ne matattar mashaya a kasar nan wato Kano. komai ka bude ka ji yadda yaro ya kashe babansa ko ya kashe kaninsa idan ba a dau mataki ba to akwai matsala.

SendShareTweetShare
Previous Post

An Yi Garkuwa Da Babban Rabaran Din Katolika A Imo

Next Post

NAFDAC Ta Kulle Kamfanonin Hada Magani Shida

RelatedPosts

Gadagi

Yadda Muke Samun Rufin Asiri Ta Sana’ar Gadagi – Muhammadu Auwal  

by Muhammad
4 days ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa, Muhammadu Auwal da aka fi sani...

Sheik Karibullah

Sheik Karibullah Ya Nada Alhaji Kabiru Sani Kwangila Khadimul Nabiyya A Taron Maulidin Gidansa

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

A ranar Lahadi ne aka gudanar da Maulidin Manzon Allah...

Buhari

Buhari Ya Yi Wa Sultan Ta’aziyyyar Rasuwar Dan Uwansa

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyar rasuwar Alhaji Abdulkadir Jeli...

Next Post
Magani

NAFDAC Ta Kulle Kamfanonin Hada Magani Shida

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version