Kwamared Sanusi Mailafiya">

Bayan Canza Hafsoshin Tsaron Kasa, Sai Kuma Me?

Yanzu dai ta faru ta kare, Shugaba Buhari ya amince da ajjiye aiki da Hafsoshin tsaron Kasar nan sukayi makon daya gabata, bayan shafe tsahon shekaru ana kira da sukar Gwamnatin Shugaba Buhari data ciresu saboda rashin tsaron daya addabi mutanen Kasar. Kusan lokacin sune muka tsinci kanmu cikin wani yanayi da bama fata ko tuna irin wannan ibtila’in muyi.
To amma wane irin kalubale ne gabansu, kuma ta ina zasu fara?. Tabbas akwai tarin ayyuka da suke gabansu don ganin cewa sun kawo dauki a irin wannan lokacin mai muni da tashin hankali, tare da tabbatarwa da duniya cewa zasu iya, kuma a shirye suke suyi komai saboda Kasarsu, kuma yardar da al’umma sukayi akansu, da mai girma Shugaban kasa tayi aiki.
Kawar da Boko Haram.
Shekaru 11 yan Boko haram sukayi suna cin duniyar su da tsinke a Arewacin Kasar nan. Yanzu ne daidai lokacin da ya kamata a taka musu birki, a kuma tabbatar an kawo karshensu. Ko burbushinsu bai kamata ya rage ba. Dole ne rundunar Sojojin Kasar nan karkashin Hafsan Sojojin Kasar Janar Attahiru da Air bice Marshal I. O Amao na Sojojin sama su tabbatar sun fatattaki yan Boko haram din. Duk da cewa a yanzu Ƙungiyar bata rike da kowane gari a jihar ta Borno, amma tabbas ya kamata a kawo karshensu, al’umma sun gaji da irin kashe-kashen da suke. Sannan su tabbatar sun kamo duk wani mai hannu a cikin wannan ta’addanci na Boko haram tare da gurfanar dashi a gaban kuliya manta sabo. Abu mafi tasiri a cikin wannan aiki da zasu sanya gaba shine ceto ragowar yaran Chibok da suka sace, duk da cewa rahotanni na nuna cewa wasu ma daga cikin yaran sun tsere ranar Juma’ar data gabata. Koma dai menene yanzu muna bukatar ganin Boko haram tazo karshe.
Garkuwa da mutane.
Garkuwa da mutane tare da neman kudin fansa kusan yanzu ya zama ruwan dare a kasar nan. Wannan ta’addanci kusan yayi matuƙar munin da kusan kullum sai kaji labarin cewa anyi awon gaba da wasu, tare da neman makudan kudade kafin a sakesu, ba’a Arewa ba, ba’a kudun ba. Tabbas wannan ma aiki ne ja a gaban sababbin rundunar tsaron Kasar nan wajen tabbatar da cewa sun kawo karshen wannan ta’addancin da ake yiwa talakawa, wanda har daliban makaranta ma basu tsira ba, kamar yadda ya faru kwanan nan a makarantar kwana ta garin Kankara.
Kisan sari ka noke a Arewacin Kasar nan.
Akwai wutar dake tashi a wasu sassan Arewacin Kasar nan, musamman jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da wasu yankuna na Jihohin Naija da Kebbi. Aiki ne babba garesu wajen ganin sun dakile wannan kashe-kashen da yan ta’addan sukeyi a wadancan Jihohin. Kusan ba’a lakume sati guda cur batare da jin mummunan labari cewar an shiga wata gundumar tare da bude musu wuta ba. Wannan kusan daidai yake da ayyukan Boko haram, zasu shiga gari da muggan makamai tare da kisan kan me uwa-da-wabi, wanda hakan yake janyo asarar al’ummar da basuji, kuma basu gani ba. Tabbas sai sun jajirce ganin cewa ko ta halin yaya sai sun kawo karshen wannan ta’addanci da yake janyo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.
Rikicin Makiyaya a Kudancin Kasar nan.
Sati biyun daya gabata ne Gwamnatin Jihar Ondo ta umarci duk wasu Fulani dake zaune a dazukan jihar ta da su bar guraren, a kokarin Gwamnan na kawo karshen sace-sacen al’umma, sai dai hakan yazo da tada jijiyar wuya a kasar, wanda har hakan ya janyo aka kai hari wa Fulanin dake cikin dazukan. Duk da cewa har fadar Shugaban kasa ta shiga al’amarin, to amma hakan zai iya janyo wata barakar da babu wanda yasan inda zata tsaya. Dole ne rundunar tsaron Kasar nan tareda sauran jami’an Gwamnatin Kasar su tashi haikam don ganin an gano bakin zaren. Musamman yadda muke fuskantar babban zabe a Kasar, wasu makiya zasu iya amfani da hakan domin assasa wani rikicin tsakanin Hausawa da Yarabawa.
Rikice-Rikicen Kabilanci.
Ministan Tsaro da sauran jami’an tsaron Kasar nan dole su tashi fafur wajen ganin wannan rikicin shima yazo karshe. Jihohi irinsu Filati, Kudancin Kaduna da sauransu dole ne a tabbatar an kawo wata masalaha dawwamammiya don kawo karshen wannan tashin-tashina wajen hakan ke janyo asarar dinbin rayuka da dukiyoyi.
Wadannan ba sune iya abubuwan da sababbin rundunar tsaron zasu fuskanta ba. Akwai kalubale na dawo da martabar tsaro wajen samun daidaito a cikin sababbin jami’an tsaron da ake dauka. Akwai magana ta dakile cin hanci da rashawa da yai katutu a rundunar tsaron ta kasa, sannan kuma akwai magana ta kawo sababbin dabaru, da sabunta makaman yaki wajen tunkarar yan ta’addan Kasar nan. Dole ne suyi kokari wajen ganin an samu sabon sauyi a tsaron Kasar nan ta kowane hali, tare da tabbatar da cimma nasara a ayyukansu.
Al’umma sun zira na mujiya ga Gwamnatin Kasar, da kuma su sababbin jami’an da aka zabo. Duk da cewa sun zo a lokacin da kowa yake neman dauki, don haka idanun al’umma yayi caa a kansu, dolene sai sun toshe kunnuwan su, sun kuma rufe idanuwansu kawai, tare da yin abubuwan da suka dace a dokance da kuma kishin kasa. Wannan shine kawai abinda zai sanya su cimma nasarori kamar yadda sukayi a baya, wacce hakan ne har ya sanya suka zo wannan bigiren.
Fatan Alheri ga Kasarmu Nijeriya. Allah ya kara hade kawunan mu.

Exit mobile version