Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za a samu tsaro a faɗin ƙasar nan, bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Talata.
Da yake magana da manema labarai bayan ganawar, Janar Shaibu, ya bayyana cewa rahoton da ya gabatar ya nuna cewa ayyukan tsaro, musamman a yankin Arewa maso Gabas, na samun gagarumar nasara.
- Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro
- Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina
Lokacin da aka tambaye shi abin da ‘yan Nijeriya za su iya tsammani a makonni masu zuwa, ya ce: “Za a samu ƙarin tsaro a faɗin ƙasar nan.”
Janar Shaibu ya bayyana cewa rahoton da ya kai wa Shugaban Ƙasa ya shafi sakamakon ziyarar aikin da ya kai yankin Arewa maso Gabas da kuma sabbin bayanai kan halin tsaro a sauran sassan ƙasar.
Ya ce: “Na zo ne na gabatar da rahoton ziyarata zuwa yankin Arewa maso Gabas, sannan na tattauna da Shugaban Ƙasa kan sauran lamuran tsaro a faɗin ƙasar na, kuma abin da na gabagar ya gamsar da shi a wannan lokaci.”














