Bayan Fitar Da Sunayen Barayin Sai Me?

08165270879

Sunayen muggan barayin gwamnati a Nijeriya da kakakin gwamnatin Tarayyar Nijeria, Lai Muhammad ya bayyana, sun tada kura kwarai matuka. Wasu ‘yan Nijeriya sun yi sambarka, wasu kuma, sai suka koma suna goyon bayan ‘yan fashin na gwamnati.

Jam’iyyar PDP da a kwanakin baya, ta fito ta tabbatar ma kanta cewa ta yi ma kanta shari’a, ta gane ita mai laifi ce, don haka tana rokon wai ‘yan Nijeriya da su yafe mata, yanzu kuma ta na cikin masu sukar lamirin fitar da jerin lis din.

‘Yan Nijeriya sun dai dade suna dakon fitowar lis din, domin kowa na son ya ga barayin da suka hana shi ingantaciyyar rayuwa, an dade ana tsokanar gwamnatin Buharin cewa wai ta na kokarin kare barayin ne. Wasu ma na ganin wai dalilin jinkirin fitowar da lis din, shi ne a baiwa barayin dama su maido wani abu daga cikin abin da suka kwasa, sannan su koma jam’iyyar APC, inda su su kuma, ba za a kai su kotu ba. Duk wannan cece ku-ce da gwamnatin ko mukarrabanta ne suka jawo mata.

To yanzu an fitar da sunaye, barayin da suka ga sunansu tuni sun fara rawar banjo, suna abin da bahaushe ke cewa da hauka ake nade tabarmar hauka. Dama kuma a al’ada ta barawo, inda ba dumu-dumu ka kama shi da kayan ka ba, to zai yi wuya bai karya ta ka ba. To ai ba mai son a ce shi barawo ne, kai ko gidanku daya da barawo ba za ka so a fada ba, in ma wani ya yi kokarin ya danganta ka da shi, za kai musu ne kawai. Yanzu ne a Nijeriya, barayi keda gata, kuma suke da bakin Magana. Yanzu za ka ga ana nada barayi sarautu, ana basu mukaman shugabancin jama’a, sabanin da, idan aka kama mutum da laifin sata, to duk randa ya kare yarinshi, ya fito, to ba zai dawo garinsu ba saboda kunya. Kuma daga ranar ya bata tarihin gidansu, ya bar ma zuri’arsu abin kunya. Amma yau ‘ya’yan barayi ne ke takama, har ma suke ji-ji-da-kai.

Wani gata da gwamnatin Buhari tai ma wadanda ake zargin sun sace lalitar kasar, shi ne da akai amfani da salon shari’a na “wadanda ake zargi” Lis din ba wai na tabbatattun barayi bane, a’a sunayen “wadanda ake zargi ne da sata”. Don haka in yanzu dayansu zai gitta ta layinku, to baka da ikon kiran shi barawo ko tsohon barawo, a’a sai dai ka ce ga “wanda ake zargi da satar kudin jama’a”.

Sai ranar da kotu ta tabbatar da laifin, wasu na ganin irin tsarin shari’ar Nijeriya kamar ma zai yi matukar wuya a taba tabbatar da laifin katon barawon gwamnati a kotu.

Ba wai kawai batun cin hanci da Rashawa da ake zargin alkalan da lauyoyi na amsa ba daga barayin domin su tsawaita shari’ar koma lalata ta da sunan “shari’a sabanin hankali” a’a, wasu hakkoki da wadanda ake zargin ke gare su, kamar na bada belin dinsu da sauran su.

Talakan Nijeriya yakan yi mamakin wai an kai Olise Metuh kotu cikin bakar motar alfarma Jif. Ko ya hango Babangida Aliyu sanye cikin faran kaftan yana fara’a ga ‘yan ma’abba baya sun biyo shi, ga tarin lauyoyi sun tsaya tsakiya, ya shigo harabar kotu, ‘yan jarida sai kokarin daukar hotonsa suke. Maimakon zuwansa kotu ya sanya shi cikin fargaba da kunya da nadama, amma sai zuwansa ya zama tamkar wani gwarzo, daga nan sai karairayin da lauyoyinsa da ‘yan jam’iyyarsa ke gaya mai na cewa ba shi da laifi, su fara shigar sa, kafin ka ce wani abu har ya fara barazana da ruba, cewa shari’arsa akwai siyasa a ciki, wai bita da kullin siyasa ne kawai.

Wata rashin kunya dake yawo shi ne, maimakon mutane su kyamaci harkar satar dukiyar jama’ a, wai sai suka kyale wadanda suka tozarta su, suka koma suna tambayoyi akan me yasa ba sunan wane ko wance? Ni a ra’ayina, ko da an ki sa sunan wane, kusan mu ‘yan Nijeriya in za mu cire son rai, mun san duk barawon dake kasar nan. Wai don sunan wane bai fito cikin lis ba, ba wai shi ne ke nuna wane ba barawo bane. A’a akwai barayi da yawa a kasar nan, wasu na kotu, wasu nama cikin ofisoshin gwamnati da dama. A karamar hukumarku, barayi nawa ka sani, wadanda suna nan suna fankama da kudin sata? To shikenan don bas u cikin jerin sunayen Lai, sai me? Wancan danmajalisar tarayyar ne, kuma barawo ne, gashi kowa ya sani, to don ba a rubuta sunan shi ba, ba zata sauya shi daga layin barayi ba.

Lallai, tunda har an fito da wasu sunaye, to dole ne nan gaba a sake fitar da sauran sunayen, domin tabbas har yanzu akwai sauran sunaye. Kuma a cire batun siyasa, yakamata duk wani barawo dake cikin jam’iyyar APC a ga sunan shi, domin jam’iyyar APC da muke gani yanzu ba mummunar jam’iyya bace, jam’iyyar ta fara bata rawarta da tsalle musamman yadda take jawarcin mutanen banza daga jam’iyyar PDP tana wanke su. Wajen yi masu wanka, ana kashe makuddan kudade. Tambaya ma anan shin daga ina kudin suka fito ne? Saboda haka idan ba ai hattara ba nan gaba kadan, dan Nijeriya zai kasa gane bambancin dake tsakanin PDP da APC domin ko’ina akwai mutanen da burinsu a siyasa bai wuce su yi kudi ba.

Yanzu mun ga an fitar da sunayen barayi, me ya rage? Fitar da sunayen barayi kawai ba zai canza komai ba a Nijeriya. Yaushe za a hukunta su? Kada mu manta akwai shari’oi wadanda ke kotunan Nijeriya tun 2007 na cin hanci da rashawa amma an kasa kamala su. Baya ga muna ganin irin hukunce-hukuncen rashin mutunci da ake yanke ma barayin gwamnati. Idan ba wannan aka sauya ba, to da wuya, bayyana sunayen barayin gwamnati yai tasiri wajen yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya. Ah, to bag a shi ba, an fito da sunayen kuma suna karyatawa, amma inda mutum ya ji shi sarka tun daga hannaye har kafa, aid a wani ba ma zai zargin wani abu ba ba. Amma yau kowa na ganin ana kai barayin gwamnati kotu, lauyoyi har turenreniya suke don su kare su, ai dole a ci gaba da wannan tafiyar da ba wanda yasan inda aka nufa.

 

Exit mobile version