Sabo Ahmad">

Bayan Samun ‘Yanci Mun Dogara Da Kanmu Wajen Neman Ilimi

Yohanna Kafarma shi ne Wazirin kabilar Jaba na yankin Zariya, da kewaye. A lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa dangane da cikar Nijeiya shekara sittin da samun milkin kai, ya ce, tun kafin zuwan Turawa al’ummar kasar nan na da hanyoyi da suke bi wajen gudanar da milki da kuma inganta rayuwarsu. Saboda haka, ko da Turawa suka shigo kasar nan sun same mu da tsari na shugabanci da kasuwanci. Abin da suka yi, mana shi ne kara bunkasa wadannan hanyoui na mu. Suka kawo mana salon shugabanci irin nasu, suka koyar da mu ilimin boko, wanda hakan ya dada bunkasa rayuwar wannan al’umma.

Saboda haka, yanzu abin da muke kara bukata shi ne, hadin kai da taunakon juna, musamman idan muka kalli rayuwar shugabannin da suka gabata, wadanda suka yi tsayuwar daka wajen ganin an samu ci gaba a wannan kasa, ba tare da nuna bambancin addini ko na siyasa ba.

Don haka, ni abin da nake ganin ya kamata mu yi a irin wannan lokaci na samun milkin kai, shi ne, mu dinga duba rayuwar shugabanninmu wadanda suka gabata da kuma irin gudummowar da suka bayar wajen bunkasa kasar nan, ba tare da nuna bambancin harshe ko na addini ba. Hada kanmu ne zai taimake mu, ba fada da juna ba. Da shugabanninmu da suka gabata, irinsu Sardauna da Owolo da Zik ba su hada kai sun ciyar da kasar nan gaba ba, da ba mu kai ga wannan ci gaban da muke da shi a hakin yanzu ba.

Don haka nake ganin a irin wannan rana ta samun ‘yanci, ya kamata mu karanta tarihin gudummowar da shugabannin da suka gabata suka bayar wajen bunkasa kasa da rayuwar al’umma.

 

Exit mobile version