Khalid Idris Doya" />

Bayan Shekara 9: Jonathan, Atiku Da Saraki Sun Jajenta Rasuwar Shugaban Kasa Marigayi Yar’Adua

Tsohon shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya jagoranci tawagar wasu muhimman mutane zuwa kai ta’aziyyar tunawa da rasuwar Marigayi Shugaban Kasa Umaru Musa Yar’Adua, tsohon mai gidansa wanda ya rasu shekaru tara da su ka shude.
Marigayi Yar’Adua dai ya koma ga mahallicinsa ne tun a ranar 5 ga watan Mayun 2010. Jonathan wanda shine mataimakinsa ya dale kan karagar mulkin shugabancin kasar bayan mutuwar Musa.
A wani sakon da ya tura a shafinsa na Twitter, Goodluck ya misalta Umaru Yar’Adua a matsayin shugaba mai gaskiya wanda yay i amfani damarsa wajen gina al’umma a lokacin da yake raye, ya shaida cewar yana da muradin hade kan ‘yan Nijeriya a lokacin da yake raye.
Tsohon shugaban kasar yake cewa; “A yau, ina tunawa da shi da irin aiyukan da ya gudanar. Mai son zaman lafiya haka ya rayu da son gina zaman lafiya a tsakanin jama’a. yana gayar son demoradiyya da mutuntata. A kowani lokaci za mu ci gaba da tunawa da irin aiyukan da aka zage damtse wajen gudanarwa. Jinjinawa ga shugaba mai gaskiya.
“Ya yi amfani da damarsa wajen yin hidima ga jama’a da ginasu cikin kauna, ya dabba’a zaman lafiya da son ganin zaman lafiya ya wadata a cikin ‘yan kasa.
“Shugaban kasa Yar’Adua mutum ne mai nagarta mai tawali’u, a kowani lokaci yana daukan muradin ci gaban kasa a matsayin muradin farko, ya tabbatar da inganta zaman lafiya da kyautata demoradiyya,” A cewar Jonathan.
Tsohon shugaban kasar ya kuma daura da cewa, “A yau, shekaru tara da rasa aboki, abokin aiki, kuma mai gidana, shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua. Shi shugaba da bai son kansa son kasa da ci gaban kasa shine a ransa,” A cewar Jonathan tsohon shugaba wanda suka mulki Nijeriya tare da marigayin.
Shi kuma a tasa jajen, tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriya Alhaji Atiku Abukakar, ya shaida cewar Nijeriya ta yi babban rashin shugaba mai murafin gina zaman lafiya da ci gaba wato Umaru Musa Yar’adua.
A takardar manema labaru da ya sanya wa hanu, ya ce “Marigayi Shugaban kasa ‘Yar’adua yana daga cikin mutanen da nake da kusanci ta kut da su. Da fari, domin dan uwan marigayin Tafidan Katsina Shehu Musa Yar’Adua, shine tauraro kuma malamina a siyasa, shine ya koyar da ni da marigayi Umaru kan hidimar siyasa.
“Na biyu kuma mun yi aiki sosai kusa da kusa a lokacin da yake gwamnan jihar Katsina a lokacin ni kuma ina mataimakin shugaban kasa tare da shugabana Olusegun Obasanjo.
“A lokacinsa, Nijeriya ta fuskaci matsalar tsaro sosai da tashin hankali, duniya ba za ta mance da shi shugaban kasa ‘Yar’adua a matsayin wanda ya taka rawa sosai wajen kawo zaman lafiya a yankin Niger Delta ta hanyar hikimarsa da sanya idonsa wanda kowa ya tabbatar da wannan,” A cewar Atiku.
Atiku ya shaida cewar marigayi ya yi kokarin daukaka daraja mai da gas a lokacin da yake shugabanci. Ya kuma shaideshi a matsayin mutum mai son bin doka da mutunta dokoki da oda, inda ya shaida cewar a lokacin da yake shugabanci Nijeriya ba ta fuskaci matsala a sashin shari’a da masu zartarwa ba domin ya bayar da hadin kai wajen mutunta doka da oda.
Atikun ya nuna cewar yana alfahari da marigayi, kana ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan Yar’adua da kuma abokansa a siyasa da addu’ar Allah kai haske makwancin mamacin.
Har-ila-yau, shima Shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki a sakon da ya wallafa ta shafin Twitter, ya misalta marigayi Umaru Musa Yar’Adua a matsayin mutum mai nagarta da bai nuna son kai wajen tafiyar da hidimar kasa ba.
Saraki ya ce: “A yau ina tunawa da mutum mai damuwa da damuwar mutane, tsohon shugaban kasar Nijeriya Umaru Musa Yar’adua, wanda ya rasu shekaru tara da suka shede. Ya bar tarihi a matsayin mutum mai nagarta, shugaba ne wanda ya taba zukatan wanda ya shugabanta. ina addu’ar Allah ta’ala ya kai haske makwancinsa ya jikansa,” a cewar Saraki.

Exit mobile version