Manyan kungiyoyin kwallon kafa Barcelona da Real Madrid zasu sake haduwa a wasan da ake yima kallon wasa mafi kayatarwa da akeyi a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a halin yanzu.
Manyan kungiyoyin biyu duka na da dadadden tarihin iya taka leda da nuna kwarewa a harkar kwallon kafa, nasarorin da suka samu a kwallo ya sa ana yimasu kallon gagarabadau kokuma ace daukakakkun kungiyoyin kwallon kafa a Duniya.
- UEFA: Mbappe Zai Jagoranci Real Madrid Yayin Da Ta Ke Fatan Kafa Sabon Tarihi A Santiago
- Copa Del Rey: Real Madrid Ta Buƙaci A Sauya Alƙalin Wasa A Karawarta Da Barcelona
Yau Asabar Barcelona da Real Madrid zasu buga wasan karshe na kofin Copa Del Rey a filin wasa na De La Cartuja dake birnin Sevilla, Barcelona ta doke Athletico Madrid da ci 5-4 a wasanni biyu da suka buga kafin ta kawo wannan matsayi.
Hakazalika Real Madrid ta fitar da Real Sociedad a wasan na kusa da na karshe da ci 5-4 a wasanni biyu da suka buga tsakaninsu, alkalin wasa Ricardo De Burgos Bengoatxea ne zai jagoranci wasan duk da rashin yarda da Real Madrid ta nuna.