Bayan Shekaru 7 Yana Ɓoye, NDLEA Ta Cafke Babban Dillalin Ƙwayoyi
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bayan Shekaru 7 Yana Ɓoye, NDLEA Ta Cafke Babban Dillalin Ƙwayoyi

byAbubakar Sulaiman
3 months ago
NDLEA

Jami’an rundunar musamman na hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) sun kama wani sanannen dillalin ƙwayoyi mai shekaru 60, mai suna Okpara Paul Chigozie, wanda ya kwashe shekaru bakwai yana guje wa hukuma, lokacin da yake ƙoƙarin aika miyagun ƙwayoyi zuwa Kudu maso Gabas da wasu yankunan Nijeriya.

An kama Okpara ne a maboyarsa da ke lamba 72, titin Michael Ojo, Isheri, Ojo, Jihar Legas a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025. A wancar safiyar da misalin ƙarfe 5:45 na safe, an cafke ɗaya daga cikin masu masa safara, Achebe Kenneth Nnamdi, mai shekaru 51, a Ilasamaja kan hanyar Apapa-Oshodi, a cikin motar Toyota Sienna.

  • Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara
  • NDLEA Ta Cafke Masu Tura Alhazai Saudiyya Domin Safarar Hodar Iblis Zuwa Kasar

NDLEA ta ce, binciken da aka yi da Karnukan gano ƙwayoyi ya gano kilo 7.6 na hodar iblis da gram 900 na methamphetamine a cikin ɓangarorin jikin motar. Bayan haka, an kai samame a gidansa inda aka gano ƙarin kilo 1.8 na wata hodar iblis da kilo 1.3 na methamphetamine.

A filin jirgin sama na MMIA, Ikeja, jami’an NDLEA tare da ma’aikatan FAAN sun cafke wani fasinja mai shirin tafiya Italy da ƙwayoyin Tramadol da Rohypnol guda 7,790. A wani samamen kuma an kama Chioba Robert Uchenna da kwayar skunk 1.70kg da aka ɓoye a cikin abincin gwangwani da ake shirin tura wa Pakistan.

Haka nan, a wani otel mai ɗakuna 20 a Kosofe, Legas, jami’ai sun cafke Obayemi Oyetade da ƙwayoyi daban-daban ciki har da 1.3kg na alawar cakuletin wiwi  da gram 900 na gummies. A Kaduna, an cafke mutum uku da kwayoyin skunk da Colorado da nauyinsu ya kai kilo 742.866.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio
Manyan Labarai

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Next Post
Mutane 2 Sun Gurfana Gaban Alƙali Kan Sare Bishiya Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano

Mutane 2 Sun Gurfana Gaban Alƙali Kan Sare Bishiya Ba Bisa Ƙa'ida Ba A Kano

LABARAI MASU NASABA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version