Mutune 70 da aka yi garkuwa da su sun samu ƴanci a Jihar Katsina, bayan yarjejeniyar sulhu da aka ƙulla da fitaccen shugaban ƴan bindiga, Isiya Kwashen Garwa. A wani faifan bidiyo da ya bayyana, Garwa ya saki mutane 40 a ƙaramar hukumar Faskari, kwanaki biyu bayan ya fara sakin wasu 30, wanda hakan ya kai adadin zuwa 70 gaba ɗaya.
Rahotanni daga mazauna yankin sun ce sakin na baya-bayan nan ya biyo bayan tattaunawa tsakanin shugabannin al’umma da sansanin Garwa, a wani mataki da ake ganin zai rage tashin hankali da hare-hare a yankin. Duk da haka, Garwa ya nuna rashin jin daɗi kan abin da ya kira sumamen Sojoji a unguwar Ruwan Godiya a lokacin Sallar Juma’a, inda ya yi zargin cewa wasu Hausawa da Fulani sun samu raunuka. Ya gargaɗi cewa irin waɗannan hare-hare na iya rusa sulhun da aka ƙulla.
- Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Sulhu Da Ƴan Bindiga A Katsina
- An Cafke Wani Magidanci Da Lafin Sojan Gona A Katsina
Hukumomin jihar ba su fitar da wata sanarwa ba kan sumamen da ake zargin ba, sai dai majiyoyin tsaro sun ce an kai hare-haren ne kan maboyar ƴan ta’adda tare da nufin kare rayukan jama’a. Mutanen da aka sako, galibinsu manoma ne da aka sace daga ƙauyukan karkara a Faskari, suna cikin kulawar likitoci da kuma binciken tsaro kafin a mayar da su wurin iyalansu.
Gwamnatin jihar ta ce tattaunawa tana daga cikin dabarun tsaro da ake amfani da su, amma ta jaddada cewa dole ne ƴan bindiga su miƙa makamansu gaba ɗaya tare da fuskantar hukunci kan laifuffukan da suka aikata.