Muhammad Maitela" />

Bayan Turmusa Trump: Biden Ya Zama Zababben Shugaban Amurka

Trump

FILE PHOTO: U.S. President Donald Trump departs on travel to the Camp David presidential retreat from the South Lawn at the White House in Washington, U.S., May 1, 2020. REUTERS/Carlos Barria/File Photo

Dan takarar Jam’iyyar Democrat a zaden Amurka, Mista Joe Biden ya lashe zaden shugaban kasar ta Amurka da a kur’iu 273, fiye da na abokin takarar sa, Donald Trump na Ripublican wanda ya samu kuri’u 214.

Hakan ya tabbatar da cewa Joe Biden shi ne shugaban kasar Amurka mai jiran gado, bayan da ya doke abokin takarar sa Donald Trump, biyo bayan gudanar da wannan zabe da ya dauki hankin duniya na ranar Talata.

Sabanin yadda yake faruwa a wasu kasashe, kwamitin yakin neman zaben shugaba Trump ya nuna abu ne mai wuya ya taya abokin takarar tasa murna.

Wannan sakamakon zaben ya nuna cewa Mista Trump shi ne shugaban da ya taba yin shugabancin Amurka falan-daya tun daga 1990.

A hasashen da masana harkokin siyasar Amurka sun nuna yadda Mista Biden ya kama hanyar lashe zaben, a lokacin da aka fara kirga kuri’un da aka jefa daga jihohi irin su Wisconsin.

Bugu da kari da gagarumar nasarar da ya samu inda ya lashe a jihar Pennsylbania wanda ya bashi damar samun kuri’un masu zabe na musamman 273 (Electoral College Botes).

Kamar yadda masu fashin baki a siyasar Amurka suka nuna, wannan shi ne zaben da jama’a suka yi wa fitar farin-dango wanda ba a taba ganin makamancin sa ba tun bayan 1900. Zabe ne wanda Mista Joe Biden ya samu kuri’u sama da miliyan 73, wadanda babu wani dan takarar da ya taba samun makamantan su a kasar Amurka.

Bugu da kari kuma, yadda tsarin zaden Amurka yake, shi ne duk dan takarar da ya fara samun kuri’un wakilai na musamman da ke zade kimanin 270, to shi ne ya samu nasara a zaden.

Saboda haka gagarumar nasarar da Biden ya samu a jihar Pennsylbania, hakan ya na nufin ya ci zaden Amurka domin kuwa ya samu karin kuri’u 20 daga wakklai ma su zabe na musamman, wanda hakan ya sa ya samu kuri’u 273, ya ma wuce 270 da ake bukata.

Amma ga dukan alamu Trump cike yake tare da niyyar maka zababben shugaban kasar gaban kuliya biyo bayan wasu korafe-korafen da Trump ya fara tun fara kirga kuri’n zaben inda yake zargin an yi aringizon alkaluma, zargin da har yanzu bai gabatar da kwararan hujjoji a kai ba.

Exit mobile version