Bayanai Na Karo Da Juna Kan Yadda Aka Kashe Shugaban ISWAP Al-Barnawi

Barnawi

Daga Abubakar Abba,

Rahotanni sun bayyana yadda aka kashe jagoran kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP a Nijeriya, Abu Musab Al-Barnawi wanda ya kasance da ga Mohammed Yusuf da ya kirkiro kungiyar Boko Haram.

Sai dai rahotanni sun yi nuni da cewa, alkaluma na ci gaba da karo da juna kan yadda aka hallaka Al-Barnawi.

Al-Barnawi dai an hallaka shi ne a Jihar Borno kuma kafin a mutuwarsa ya kasance jagoran ‘yan a ware na kungiyar Boko Haram, inda aka ruwaito cewa kungiyar ISIS ce ta zabo Al-Barnawi domin ya jagoranci yankin Tafkin Chadi.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa, Al-Barnawi an kashe shi ne a watan Agustar 2021 Agusta, sai dai akwai bayanai guda biyu da ke cin karo da juna kan yadda aka hallaka Al-Barnawi, inda bayani na farko ke cewa, dakarun sooji da ke a fagen fama a yankin Arewa Maso Gabas ne suka kashe shi, a daya bangaren bayanin kuwa ke nuna cewa, an hallaka Al-Barnawi ne a yayin wata artabu da ya yi da wasu ‘ya’yan Kungiyar ISWAP da suke gaba da shi.

Bugu da kari, a bayanan na farko, wadanda kuma suka fito daga wasu jami’an tsaro na soji, sun nuna cewa a wani samame ne da dakarun sojin suka kai suka samu nasarar kashe Al-Barnawi, inda a lokaci samamen har wasu manyan jagororin Kungiyar ISWAP hudu zuwa biyar da ke biyayya ga Al-Barnawi suma dakarun sojin suka hallaka su.

A cewar majiyar, an hallaka Al-Barnawi ne a yakin Bula Yobe da ke da iyaka da jihohin  Borno da Yobe daura da Mobbar da  Abadam da ta bulla zuwa yankin Tafkin Chadi.

Har ila yau, wata majiya ta bayyana cewa, dakarun sojin sun  tare Al-Barnawi ne a Yale, Bama, mahadar Banki zuwa  yankin Kashimbri-Gulumba, inda suka hallaka shi, yayn da wata majiyar ta ce wasu ‘yan Kungiyar ISWAP ne suka  kashe Al-Barnawi saboda rikicin shugabanci.

A cewar majiyar, rikicin shugabanci a kungiyar ta yi kamari ne a tsakanin 14 zuwa 26 ga watan Agusta na 2021, inda rikicin a tsakanunsu  ya yi sanadiyyar rasa rayukan masu yawa musamman ma kwamadojin bangarorin guda biyu da ke yakar juna.

Hakazakika, wata majiyar ta ce bangaren ‘ya’yan kungiyar da ke yakar Al-Barnawi sun gayyato  wasu ‘yan ta’adda daga Nahiyar Afirka ta Tsakiya don a tunbuke Al-Barnawi daga ci gaba da shugabancin kungiyar, inda kuma suka ci nasara.

Masana a fannin harkokin tsaro a kasar nan sun yi hasashen cewa mutuwar Al-Barnawi a watan Agustar 2021 da kuma mutuwar Shekau a watan Mayun 2021, ana ganin samun wata babbar nasara ce a ci gaba da yaki da ta’addanci musamman a yankin Arewa Maso Gabas.

Sai dai, Rundunar Sojin Nijeriya ba ta sanar da tabbatar da kashe Al-Barnawi ba haka kuma ba ta karyata cewa hallaka Al-Barnawi da wasu manyan kwamandojin kungiyoyin Boko Haram da na ISWAP ba.

Mai yuwa, rundunar  na son kauce wa maimaita fitar da bayanai ne da ta yi a baya kan kashe shugaban Kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau wanda daga baya ya sake bayyana.

An ruwaito cewa, Daraktan Yada Labarai na Shalkwatar Tsaro ta Kasa, Majo Janar Benjamin Sawyer bai tabbatar da cewa sun hallaka Al-Barnawi ba, domin dakarun sojin ba su da wata hadaka da ‘ya’yan kungiyar ta ‘yan ta’adda ba.

Benjamin Sawyer ya ce, “Idan akwai wata rashin jituwa a tsakanin sansanin ‘yan Kungiyar Boko Haram ba za mu sani ba, a koda yaushe ‘yan jarida ne ke fitar da bayanai idan har akwai sabani tsakanin kungiyar ISWAP da Boko Haram, amma ba mu ba, domin mu ba a sansaninsu muke ba.”

Ya ci gaba da cewa, Al-Barnawi  na da wani faifan murya a harshen Kanuri da ke tabbatar da mutuwar Shekau da kuma nasarar da bangaren  Al-Barnawi  ya samu.

A cewarsa, wannnan shi ne abin da Al-Barnawi ya fada a cikin faifan muryar mai tsawon minti 28. Inda ya ce,”Shi Shekau bai taba tsammanin hakan za ta rutsa da shi ba  ko da kuwa a cikin mafarkinsa, amma gashi, bisa ikon Allah mun tarwtasa rayuwarsa”.

Benjamin Sawyer ya ci gaba da cewa, Al-Barnawi ya shiga cikin rudani lokacin da ya arce zuwa jeji, inda ya shafe kwanuka biyar yana watangaririya a jejin.

A cewar Benjamin, “Dakarunmu sun bukaci Al-Barnawi da ya mika wuya don a hukunta shi, inda muka ci gaba da ba shi tabbacin cewa  ba wai mun fito don kashe shi ba ne, amma sai dai ya nuna  jayayya a zamansa na tantiri, ya gwammace ya mutu maimakon ya mika wuya.

An ruwaito cewa, Shekau ya kashe kansa ne da bam bayan ya lura cewa mayakan Kungiyar ISWAP na yunkurin kama shi a raye.

 

Exit mobile version