Idris Aliyu Daudawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KIWON LAFIYA

Bayanan Masana Ilmin Kimiyya Dangane Da Kayyade Iyali

by Idris Aliyu Daudawa
February 17, 2021
in KIWON LAFIYA
5 min read
Tazarar Haihuwa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Mene ne ƙayyade iyali?

Shi al’amari kaiyade iyali ko bayar da tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wannan wani mataki ne da ma’aurata  su kan dauka don hana mace daukar ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko kayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa, ko dai ma don wasu dalilai na daban, kamar abin da ya shafi lafiyar uwa da makamantan su. Duk da cewa akwai ce-ce-ku-ce da yawa game da halarcin ko rashin halarcin tsarin kayyade iyalin, amma al’amarin ne da ya kamata duk ma’aurata su kasance sun samu ilimi game da shi don watakila wata rana zai masu amfani.
Amma babban abu mafi muhimmanci sh ine a duk lokacin da ma’aurata suka yi niyyar kayyade iyalinsu to su tafi wurin kwararren likita don samun shawarwari ta yadda zai zama an yi dace.

samndaads

Ire-iren hanyoyin kayyade iyali
Da farko yana da kyau ma’aurata su sani akwai hanyoyi guda biyu da ake bi domin kayyade iyali. Wadannan hanyoyin kuwa su ne:

Hanyoyin Hanawa Ba Tare Da Shan Magani Ba
Wadannan sune hanyoyi da ake bi ba tare da shan magani ko kuma saka wani abu  ba a jikin mace ko namiji ba domin hana daukar ciki
:
Yadda ake daukar ciki
A mahaifa ko uterus a Turance akwai wasu wurare guda biyu gefe da gefe da ake kira da suna obaries (maikaratu na iya duba hoton da ke sama don fahimtar wannan bayani). Wadannan obaries din sune mazaunar kwayayen halitta na mace. Duk wata da akwai daya ko fiye na kwayayen da za su fito daga obary (obulation) su bi wata hanya da ake kira da suna fallopian tube, anan ne idan akwai maniyi sai su hadu. Wannan haduwa ta kwai da maniyyi shi ake kira da suna fertilization. To wannan kwan  sai ya gangaro gefen da ciki ke zama na mahaifa ya dasu wannan shi ne mafarin cikin ke nan.
To amma wannan kwan ko kwayaye na rayuwa ne na tsawon awa 12 zuwa 24 (wasu sun ce ya kan kai har kwana uku) idan bai samu maniyyin namiji ba, sai ya lalace. Daganan shi kuma maniyyi na iya zama a jikin mace har na tsawon kwana shida ne ko bakwai tsanani kafin ya lalace. Saboda haka idan mace ta sadu da na miji maniyyinsa na iya zama har na kwana shidda wanda hakan na nufi a wannan tsakanin idan kwanta ya fito to za ta iya daukar ciki ke nan.

  1. Barin saduwa a lokutan da mace za ta iya daukar ciki wato idan tana obulating
    Ga yadda ake bin diddigin lukutan da mace za ta iya yin ciki. Mace ta fara kirga kwanaki, tun daga ranar farko da ta fara al’ada har kwana sha hudu. Bayan kwana sha huɗun nan sai a fara kirga, rana ta sha biyar har zuwa sha takwas ko kuwa sha tara to wadannan kwanaki su ne lokacin da mace za ta iya daukar ciki. Amma wasu lokutan ya danganta ne daga mace zuwa mace da sanin lokacin obulation da kuma yanayi da mace ke ciki. Saboda haka yana da kyau a ziyarci likita domin samun cikakken bayanin yadda mace za ta bi diddikin daukar ciki .

Wasu hanyoyin hana daukar ciki na zamani sun hada da:
Duba yadda yanayin jiki yake  a kullu  domin sanin lokacin shigar ciki. Domin a lokacin obulation yanayin jikin na tashi kadan kamar da degree 0.2. Sanin wannan zai taimaka wajen daukar matakin daya dace don hana daukar ciki.
Duba canji da ake samu na cerbical mucus (wato farin ruwa mai yauki-yauki da ke fitowa a gaban mace). Idan mace na obulating shi wannan ruwa na canzawa. Ya kamata idan mace tana son gwada wannan hanyar ta ziyarci kwararru akan al’amarin kiwon lafiya daya shafi mata don a koya mata yadda zata yi da kuma yadda zata iya banbance wannan cerbical mucus din.
.
Hanya ta zamani
Wadannan su ne hanyoyi daban-daban da ake bi don samun nasara akan kayyade iyali ta hanyar shan magani ko kuma ta hanyar saka wani abu. Hanyoyin suna da yawa, amma ga wasu daga cikinsu kamar haka:
1.Intrauterine debice (IUD)
IUD wata ‘yar karamar roba ce wadda tayi kama da T da ake sakawa a mahaifar mace don ta hana maniiyin namiji haduwa da kwai ko kuma idan har ma sun hadun ba zai bawa kwan damar shiga ita mahaifar. Wannan hanyar masana sun tabbatar  da cewar idan an yi ta dakyau tana yin amfani kamar kashi 99 cikin 100 wajen hana daukar ciki. Ta kan iya zama har na tsawon shekara 5 zuwa10 a jikin mace. Bugu da kari kuma ana iya cire ta a kowanne lokaci idan ana so. Kuma da zarar an cire ta za a iya daukar ciki nan take.
An tabbatar da cewa wannan hanyar bata da wani hatsari sosai ga mace. Amma sai dai dan abinda ba za a rasa ba wani lokacin mace na iya samun kamuwa da wata cuta, wato kwayoyin cuta, hakanan ma ya kan iya kara yawan jinin al’ada da kuma tsawonsa musamman ma a watanni 6 na farkon sakawa. Idan mace na bukatar amfani da wannan hanyar ta tabbatar da ta samu kwararriya ko kwararren likita domin ta saka mata sannan ta tautauna da likitar don sanin abin yi da kuma yadda abin ke aiki.
Magani ne na kwaya da mace za ta rika sha mafi sau da yawa har na kwana 21 a jere kuma a lokaci daya a kullum sannan ta tsaya na kwana bakwai, bata shan maganin. Haka za ta riƙa yi duk wata. Wannan pills din na saka jiki ya rika sakin wasu kwayoyin halitta, hormones ne da zai hana mace daukar ciki. Wannan hanyar tsarin kayyade iyalin wani lokacin yana da wuya domin dole mace ta tuna kullum ta sha kwayan yadda ya kamata. Idan kuma a ka manta yana iya rage kaifin aikin maganin. An ce shi wannan hanyar ya na aiki kamar kashi 99 cikin 1000 shi ma idan aka bi shi yadda ya kamata
Wani lokaci, shan pills din kan iya haifar da jin amai ko gudawa, da kuma (canjin yanayi) da dai wasu yanayi na rashin jin dadi musammam a lokacin da aka fara amfani da pills din ba a jimawa ba.

  1. Contraceptibe implants
    Wannan wata hanya ce da ake dasa wata roba karama a hannnun mace. Shi wannan roba zai rika fidda wani hormone da ake kira da suna progestogen a cikin jini ne da zai hana mace daukan ciki. Yana iya zama a jikin mace har na tsawon shekara 3. Amma ana iya cire shi duk lokacin da ake bukata a asibiti. An tabbatar shi ma wannan hanyar tsarin kayyade iyali na amfani wajen kashi 99 cikin 100 ko fiye wajen hana daukan ciki. Matsalolon da akan hadu dasu sun hada canjin yanayi, amai, wani lokacin ya kan hana mace al’ada gaba daya, ko kuma al’adarta ta rikice da ma

  2. Diaphragm or cap
    Wata roba ce mai kama da hula da mace kan sa lokacin saduwa don hana maniyi shiga mahaifarta. Ana amfani da ita ne tare da wani gel da ake kira da suna spermicide. Amfani da diaphragm na kare mace da daukar ciki da kashi 92 ko fiye idan anyi yadda ya kamata.

  3. Allurar hana daukar ciki
    Allura ce da akan yi wa mace don ta hana ta daukar ciki. Yawancin allurar na aiki na tsawan mako 8 zuwa mako 13. Shi wannnan hanyar koda an bar yin allurar yana iya kaiwa shekara kafin mace ta iya sake daukar ciki. Sannan ya kan iya kawo matsalar al’ada ko ma tsaida shi yin ita al’adar gaba daya. Babbar matsalarta ita ce  sun hada ta da, sa ciwon kai, kara kiba da sauransu.
    Wasu hanyoyin sun hada da amfani da kwaroron roba wato condom na maza da na mata yayin saduwa, da contraceptibe sponges da dai sauransu.

SendShareTweetShare
Previous Post

An Dawo Zagaye Na Biyu Na Gasar Kofin Zakarun Turai

Next Post

Za Mu Yi Hukuncin Kisa Ga  Wanda Aka Kama Da Laifin Fyade – Gwamnan Nasarawa

RelatedPosts

Me Ke Kawo Karkacewar Baki Kwatsam?

Me Ke Kawo Karkacewar Baki Kwatsam?

by Idris Aliyu Daudawa
1 day ago
0

Daga Mustapha Wakili da Muhammad Zahraddin Shanyewar barin fuska larura...

Illolin Shan Ruwa Mai Sanyi Yau Da Gobe

Ruwa Da Amfaninsa A Jikin Dan Adam

by Idris Aliyu Daudawa
2 days ago
0

Amfanin ruwa guda tara a jikin dan Adam idan ya...

Ciwon

Yanzu Ciwon Sikari Bai Bar Kowa Ba

by Idris Aliyu Daudawa
3 days ago
0

Likita, wanda yake lura da masu fama da ciwon sikari...

Next Post

Za Mu Yi Hukuncin Kisa Ga  Wanda Aka Kama Da Laifin Fyade – Gwamnan Nasarawa

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version