Wani Birgediya Janar na Sojan Nijeriya mai ritaya, Idris Bello, ya bayyna cewa, kyakkyawan bayanan sirri da sojojin Nijeriya ke samu na iya kawo karshen yakin da ake yi da Boko Haram.
Ya fada wa manema labarai a wata hira cewa, “a kan batun kame da gurfanar da wasu ‘yan Nijeriya a Dubai da ake zargi da hada wa Boko Haram kudade masu yawa. Wannan wani abu ne na farin ciki matuka domin zai taimaka wajen karya lagon maharan. Ta wannan aikin, an toshe babbar hanyar samun kudaden su har abada don haka zasu sami karancin kudaden sayan makamai da kayan aiki.”
“Duk an cimmawa wannan ne saboda kyakkyawan tattara bayanan sirri da aka yi na tsawon lokaci. Wannan wata alama ce da ke nuna irin muhimmancin da tattara bayanan sirri ke da shi wajen yaki da tayar da kayar baya da sauran kalubalen tsaro.”
“Batun Amurka na amfani da sararin samaniyar Nijeriya don kubutar da wani ba’amurke da aka sace, shi ma yana da alaka da kyakkyawan hankali. Dole ne Amurkawa su sa ido kan halin da ake ciki na dan lokaci ta amfani da mutane da na’ura wajen samun sahihan bayanan sirri. An samu saukin gudanar da aikin ne ta kebe wurin. Kuma da ace yanki mai yawan jama’a wannan zai yi matukar wuya. Amurkawa sun kuma yi aiki tare da hadin gwiwar hukumomin tsaron Nijeriya,” in ji shi.