Connect with us

KIWON LAFIYA

Bayani Kan Cututtuka Masu Yad o (Trasmitte Disesses)

Published

on

Ya ‘yan uwa masu karatu, in ana biye da mu muna bayani ne kan maganar cutar ciwon sanyi wanda ake d auka ta hanyar jima’i da turawa suke ce da ita ‘Transmitted disease’. Wadda a larabce kuma suke ce mata “Al’amradhul jinsiyya attanasiliyya” wanda awurin likitocin musulmi kuma suke ce mata ‘Habbal ifraji’ kamar yadda Imamu siyud i da Ibnu Baitar suka kira ta.

Shi wannan ciwo na sanyi ya zo da had arin gaske, da yake d auke kusan duk wata rayuwa ta farjin mutane, tunda akan had u da ganin farin ruwa a gaba ko kurarraji ko tsiro da wani wari, ko d ad ewa, ko rashin jin gamsuwa ga mace da rashin sha’awa. Uwa uba ma ya kan lalata maniyyin mace ko na namiji, don haka sai ka ga babu haihuwa, yayin da wani lokaci ya kan taba sashin jikin ma.

Don haka sai ka ji baki na wari, lebe na d ad ewa, ko rashin sha’awa, matse-matsi yana kaikayi, ciki babu lafiya, da dai sauransu.

Ya ku ‘yan uwa ku sani muna yi maku wannan bayani ne don ku san ciwon ku guje shi, kuma in mun ji cewa akwai alamunsa a tattare da mu, mu yi gaggawar neman magani musamman maganin musuluci da yake magance cuta tun daga tushe, domin lafiya ita ce rayuwar d an Adam, don bayan imani da Allah Ta’alah sai ita.

Manzon Allah yake cewa “Innakum lan tu’utu sha’an ba’ada kaliamtul’iklas mislul afiya, salullaha afiya”.

Wato manzon Allah yake cewa “ Ku babu wani abu da za a baku da ya fi lafiya”. A wani Hadisi yake cewa “Salullaha afiyata fiddunya wal akhira”. Wato “Ku roki Allah lafiya aduniya da lahirarku”. Duka wad annan hadisai sun zo cikin (Ahadisul Mukhtar) kamar yadda Dallak yake fad a a wani baitin wakarsa yake cewa “ Ma an amallahu ala Abdihi bi ni’imatin aufa minal a fiya, wa kullu man ufiya fi jismihi fahuwa fi ishatirradhiya”.

Wato babu wata ni’imah da Allah Ta’alah zai ni’imta bawansa da ita makar lafiya”. Saboda haka “Duk wanda aka ba wa lafiya yana cikin rauwa ni’imtacciya”.

To shi wannan ciwo na sanyi ya kasu kashi 16, wasu masu bincike suna kai shi 21, kuma ko wane kashi da irin alamunsa, kuma da maganinsa. Saboda haka za mu fara d aukarsu d aya bayan d aya mu yi bayanisu’Tafsilan’ in sha Allahu.

Na farko shi ne (Maradhussaialah) wanda turawa suke ce da shi Gonoriya, shi irin wannan nau’i na ciwon sanyi yana da had ari matuka idamn ba a gane shi da wuri ba, ko kuma in ba a bashi kulawa ta musamman ba.

Tarihin wannan ciwo dad ad d e ne kamar yadda mafiya masana tarihi suka fad a, misali daga cikin masana masu binciken zamani akwai wani mai suna Swido da ya rayu 1748 zuwa 1824 da yayi magana akanta cikin rubce-rubucensa, amma masanan duniya sun yi bincike na zamani, inda suka tabbatar da ita, kuma suka sawa a kwayar cutar suna (Gonocus neisser) a 1882, kamar yadda Samir Shaikani ya kawo a littafinsa mai suna (Al alfiyatussaniyya).

kuma duk alamunta da suke bayyana in ta kama mutum sun bayyana tun a zamanin Fir’auna, kamar yadda aka samu a rubutunsu Abkirad da masana Chanis da Hindu, kuma tsawon zamanin wasu suna ganin kamar ita ce Zuhuri wato Sifilis, wadda za mu zo  mu yi magana a kanta nan gaba in sha Allahu.

 

  • Bayani ciwon Sanyi Na Kandida

Shi wannan ciwon sanyi mai suna Kandida maza su kan d auka a wurin matansu, sai dai a mafi yawa bai fiya nuna alama a jikinsu ba, sai kad an ake samu wad anda suke d an jin zafi, wanda su ke ganin wani abu da iyalinsu. Ko kuma wani farin ruwa ya fita daga gabansu musamman in ana saduwa.

Shi wannan ciwon sanyi na Kandida, yana da had arin gaske, domin da zarar ya fara zub da wannan farin ruwan da mata suke gani kamar ko wace mace yake, sai gabansu yayi sanyi maimakon d imi. Saboda haka  ba zai gamsar da mijinsu ba. Wadda take ganin haka, ta yi gaggawar zuwa don a bata magani ta warke da iznin Allah Ta’alah.

Sannan kuma wani karin bayani game da farin ruwan da matan ke a gabansu, wanda dole shi ma sai magance shi shi ne, wanda yake haifuwa sakamakon ciwon sukari wato ‘Diyabitis’ da rashin isasshen jini a jiki, wato jiki baya samun abincin da yake so, saboda haka yawan cin kaza me mai yana taimakawa, ko kuma masu ciwon Sikila, ko kuma masu amfani magungunan hana haifuwa kuma jiki bnai daidaita da shi ba. Ko kuma ciwon Daji wato ‘Cancer’ ko kuma magugunan bature da ake sha don sabe kumburi, ko yayin da ake da ciki wato mai juna biyu, yana daga alamun wannan ciwo na Kandida ga mata, sai su daina jin d and anon saduwa yayin saduwar.

Fitar farin ruwa kamar yadda muka yi bayani a baya, sai in ya had u da rashin tsafta sosai, ya kan haifar da kaikayi, kuma wani lokacin ko da kwai tsaftar yak an haifar. Sannan kuma farin ruwa ya kan cure ya dunkule kaga yana fita a cuccure guda-guda, wani lokaci gari-gari, kuma yak an iya cushewa a cikin mahaifa, saboda haka sai a kasa samun ciki don ba zai bar maniyyin namiji ya wuce ba. Kuma ya kan haifar da ciwon mara mai tsanani musamman lokacin al’ada ayi ta magani ba ta warke ba.

Amma da an yi maganai wannan ciwon Kandida sai ta warke ka ga ta daina, sannan ya kan haifar da d ad ewar a gaba, wani lokacin har da cinyoyi, ya hana bacci saboda kaikayin da yake yi in an kwanta. Ga maza ma ya kan haifar da kumburi a mara, da jin zafi yayin fitsari, amma su a mafi yawa sai rana ta dake su, duk da cewa su ma matan suka had u da jin zafin fitsarin in rana ta dake su, kuma mafi yawa sakamakon ciwon sanyin ne Kandida.

Kuma ya kan sa namiji karfinsa ya ragu, ko ma ya daina sha’awa sai da kyar, don akwai wanda aka yi fama da shi, yana jin wannan zafin fitsarin har ma aka yi ta yi masa gwaje-gwaje a asibiti ba a ga komai ba. Haka likitoci sukai ta kokari akansa amma bai warke ba.

To da ya zo wajenmu da cewa aljanu ne, da muka bincika sai muka ga ba shi da matsalar aljanu, nan muma mu kai ta ba shi namu kokarin amma bai warke ba. A karshe dai muka yi addu’ar neman dacewa ga Allah Ta’alah, Allah ya amsa mana sannan mu ka d auki maganin maganin shi wannan Kandida muka bashi, ya warke sarai ya dena kamar ma bai taba yi ba.

Ya ‘yan’uwa ana so yayin da mutum yake maganin shi wannan ciwo na Kandida, yayi da shi da iyalansa, kuma duk abinda ake amfani da shi a jiki musamman wanda yake had uwa da gaba kamar Pants, da dai sauransu a wanke su da ruwan d imin da aka sawa gishiri ko Detol, saboda duk wanda ya zo wurinmu ya karbi magani ciwon sanyi ko da mun manta ba mu gaya masa ba, to ya tuna yayi amfani wannan shawarar tamu.

Haka ‘yan makaranta su dinga yin dabarar biyan bukatarsu a ban d aki don kar su d auki wannan ciwon sanyi na Kandida, da sauran cututtukan sanyi da mu ka yi bayani a baya da wad anda za mu yi su nan gaba in Allah ya so.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: