Connect with us

Uncategorized

Bayanin Taron Manema Labarai Na Kasa Da Kasa Na Gaggawa Da Shugaban Jam’iyyar NCP, Alhaji Abdulmumini Shehu Sani Ya Yi Ranar 3 Ga Satumba, 2018 A Katsina

Published

on

Na kirawo ku ne zuwa ga wannan taron manema labarai na gaggawa don in sanar da ku da kuma jama’ar jihar Katsina da al’ummar Nijeriya da ma na kasa da kasa kan irin mummunar zamba, wasoson kudin jama’a da wasu manya a gwamnatin Jihar Katsina suka yi tun bayan hawansu kujerar mulkin jihar a watan Mayu 2015.

Wannan batu ba zargi ne mara tushe ba, amma gaskiyar da take tattare da hujjojin da ba mai iya musanta su. Saboda amanar da na yi cewa wannan zambar bai kamata a share su kuma a binne su ba, amma a bincike su, kuma wadanda suka aikata su a gabatar da su gaban Kuliya a yanzu ko a nan gaba, tuni har na mika wannan bayanin ga Hukumar yaki da cin hanci da almundahana ta kasa, wato EFCC, kamar yadda zan bayyana muku a yanzu.

Abin da ke tafe wasu misalan irin laifuffukan yi wa tattalin arziki zagon kasa na wasu manyan jami’an gwamnatin ne:

 1. Fitar da wasu kudade da suka haura Naira biliyan 3 daga Asusun Sure-P da ke bankin Access Bank da wasu bankunan daga watan Yunin 2015 zuwa Disamban 2015, wanda ya saba wa doka don amfanin wasu jami’an gwamnatinsa, wanda ina da kwararan shaidun fid da kudaden ba tare da shaidar yin wani aiki da su don jama’a ba.
 2. Bayar da kwangila ta Naira biliyan 2.8 don samar da takin zamani ba tare da wani tanadin haka daga kasafin kudi, ko Hukumar neman kwangila ko amincewar Majalisar zartarwar jihar ba, wanda ya wuce iyakar da Gwamna zai iya badawa, kuma ba a samar da takin zamanin ba. Maimakon haka takin zamanin da gwamnatin da ta gabata ta taskace ne aka rarraba.
 3. Zambar karkatar da wasu kudade sama da Naira biliyan 2.5 daga Asusun Hukumar kula da gidaje na jihar da kuma wasu kudade mallakin jihar da Kananan Hukumomi, wanda yin hakan ya saba wa dokokin jihar da kuma ka’idojin gudanar da aiki.
 4. Hayar da aka yi wa sojoji na wani gini mai suna Karama House da ke kan titin Hasssan Usman Katsina a kan kudin da ya wuce hankali na Naira miliyan 750 a shekara, tare da yi wa gidan kwaskwarima a kan Naira miliyan 250, amma kuma aka mai da ginin don mukarraban gwamnati.
 5. Fitarwa da kuma karkatar da wasu kudi Naira miliyan 589 ba bisa ka’ida ba da wani Kabiru Faskari (Kebram) ya yi da sunan ciyarwar watan Ramadan, wanda amma aka ba matar wani babban jami’í da wani mutum, wanda yake na hannun daman Gwamna ne, wanda ya taimaka masa fid da kudin.
 6. Wasoso, karkatarwa da ma satar Naira biliyan 3.6 tsaba a 2016 da gwamna da wasu jami’an Ma’aikatar kudi ta jihar suka yi daga wani Asusun kudin tsaro, wanda hakan ya saba wa tanaje-tanajen doka, ta hanyar fid da kudin tsakanin Naira miliyan 20 zuwa Naira miliyan 300 a raneku mabambanta a cikin 2016, kudaden da kuma ba a bai wa jami’an tsaron ba, amma suka rarraba a tsakanin su. Irin wannan fitar da kudin sun hada da:
 7. Naira miliyan 88 tsaba don nuna karfin jami’an tsaro a ranar 25/2/2016.
 8. Naira miliyan 270 tsaba don sa ido na tsaro a Kananan Hukumomi 34 na jihar ranar 6/4/2016.
 9. Naira miliyan 250 aka fitar tsaba ran 18/6/2016 kan wai rangadin tsaro wanda yake na boge ne.
 10. Kudi Naira miliyan 325 aka fitar ran 26/6/2016 da sunan rangadin tsaro a birnin Katsina, wanda ba a yi ba, aka rabe kudin tsakanin gwamna da sauran mukarrabai.
 11. Kudi tsaba Naira miliyan 74 aka ba Kwamishinan ’yansandan jihar na lokacin a ranar 2/5/2015.
 12. An fitar da Naira miliyan 150 a ranar 8/10/2016 da zimmar raba wa jami’an tsaron Shugaba Buhari.
 13. An fitar da Naira miliyan 110 tsaba ra 9/10/2016 bisa zimmar za a ba Kwamandan bataliya ta 35 na sojojin Nijeriya.
 14. An fitar da Naira miliyan 150 tsaba ranar 5/5/2016 da zimmar za a tattauna da shugabannin addini, wadanda karshe ba su sami ko da Naira miliyan biyar ba.
 15. Naira miliyan 50 aka fitar da sunan taimakon AIG Shiyya ta daya ran 11/2/2016.
 16. Naira miliyan 20 aka fitar da sunan biyan ’yansanda mobayil goma da ke gadin Lambar Rimi Wind, alhali jami’an tsaron suna karbar kasa da Naira miliyan daya ne duk wata.
 17. Sama da Naira miliyan 318 aka fitar da sunan an kashe su don tarbar ’yan siyasar da suka canza sheka a gangamin APC da biyan kudin hayan ofis-ofis na APC.

 

WASU MISALAN ZARGIN ZAMBA

Kudin Paris Club: Gwamnatin jihar Katsina ta karbi jimla Naira biliyan 14.5 a matsayin kudin Paris Club a farkon 2017, amma wani bangare na kudin raba shi kawai aka yi tamkar ganima a tsakanin jami’an gwamnatin jihar. Akwai hujjojin da ba a shakkunsu da ke nuna yadda aka yi rabon tsakanin jami’an gwamnatin jihar, ’yan majalisa da abokina tafiyar gwamnatin.

Kudin taimakon gwamnati: Sama da Naira biliyan 11 ne gwamnatin jihar Katsina ta karba da zimmar biyan kudin albashi da ma’aikatan jihar ke bi da kuma kudin ariyas da gwamnatin da ta gabata ba ta biya ba. Amma da ta bayyana cewa ba wani albashi da ma’aikata ke bi, sai gwamnatin jihar ta yi karyar cewa ta biya bashin kudin fensho da su. Hujjojin da ba sa karya sun nuna cewa kudin an aje su ne a bankin don samun kudin ruwa da aka yi watandar su tsakanin manyan jami’an gwamnati, su kuma ’yan fenshon aka rika biyan su da kadan da kadan.

Bayar da hayar gonar Shonghai Farms: Gwamnatin da ta gabata ta kashe biliyoyin Naira don gina gonar da ake kira Shanghai Farms, inda ake horar da matasa noma da bai wa manoma dabarun noma da samar da abinci da hatsi don bunkasa tattalin arzikin jihar. Amma wannan gwamnatin mai ci sai ta bayar da wannan wuri haya da kuma filin noma hekta 10,000 da ke kewayen Zobe Dam ga kamfain Dangote Group a kan kudi Naira miliyan 500, abin da ya watsar da manoma ’yan jihar Katsina da matasan da ke samun horo, wanda hakan ya hana jihar Katsina cin gajiyar amfanin da za a samu daga gonar. Dadin dadawa, gwamnatin jihar ba za ta iya yin bayanin yadda aka yi da kudin hayar da aka biya ba ko za a biya bisa kudurin gwamnatin na baje komai a kan faife don jama’a su tantance ba.

Manufar tsare gaskiya: Gwamnatin Masari ya zuwa yanzu ita ce gwamnatin da ta fi tsare gaskiya a tarihin jihar Katsina. Sai dai kuma albasa ba ta yi halin ruwa ba, don kuwa sabanin alkawurin zabe da gwamna ya yi sai ga shi yana tafiyar da gwamnati ce wacce harkokin kudinta suke lullube cikin sirri da tafka almundahana.

Kwamitin rikon kwarya da aka kakkafa a Kananan Hukumomi ba an kafa su ba ne don kusanto da gwamnati ga jama’a, amma sai don samar da wata dama na yin wasoson biliyoyin Naira daga asusun ajiyar Kananan Hukumomin da kuma halasta ci gaba da kwashe kudin baitulmalin Kananan jihohin. Hujjoji suna nan a kasa kan yadda wadannan Kwamitoci aka rika tilasta su sanya hannu kan fid da wasu kudade da aka yi a baya daga kudin masu biyan haraji a jihar.

KAMMALAWA

Dangane da EFCC: ’Yan Magana na cewa, “jinkirta adalci, tamkar hana adalci ne.” Kawo yanzu na gabatar da hujjoji na koke-koke ga EFCC a kan laifuffukan almundahana da jami’an gwamnatin jihar Katsina suka aikata. Amma har ya zuwa yau din nan babu wani takamaimen matakin da aka dauka don binciken wadannan zarge-zarge ko gabatar da wadanda ake zargi gaban Kuliya. Don haka ina kalubalantar EFCC da ta kama aiki gadan-gadan don ceto hurumin da aka ba ta na bincika da hukunta masu yi wa tattalin arziki zagon kasa daga jami’an gwamnatin jihar Katsina. Wannan mummunan wasoson kudin jama’a da ake yi a jihar Katsina babban barazana ne ga tsaron kasa, kuma kullum kara muni yake yi.

SA HANNU:

Abdulmumini Shehu Sani
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: