Wata kotun Nijeriya ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Saminu Turaki bayan hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta’annati (EFCC) ta kama shi bisa zargin wawure naira biliyan 36 a lokacin da yake kan mulkin jihar.
An dai bayar da belinsa ne bayan wasu mutum biyu mazauna Abuja sun tsaya masa.
Jim kadan, kotun ta bukaci tsohon gwamnan ya rika kai kansa ofishin hukumar EFCC duk bayan mako biyu.